Gwamnonin Najeriya Sun Yi Allah Wadai da Tashin Bam a Jihar Zamfara
- Gwamnonin jihohin Najeriya sun yi tir da tashin bam da ya faru a kan titin Ɗansadau a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma
- Gwamnonin sun bayyana lamarin a matsayin babban abin takaici da yunƙurin wasu miyagu na ƙara firgita ƴan Najeriya
- Sun kuma jajantawa al'umma da gwamnatin Zamfara, sannan sun bukaci dakarun sojoji su kara dagewa wajen kawo karshen matsalar tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Zamfara - Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta jajantawa al’umma da gwamnatin jihar Zamfara bisa fashewar wani bam a kan titin Ɗansadau.
Fashewar ta faru ne a lokacin da wata motar haya ta taka bam ɗin a daidai garin Ƴar Tasha da ke yankin karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa akalla mutum shida ne suka rasa rayukansu sakamakon tashin bam wanda ake zargin ƴan ta'adda suka dasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnonin Najeriya sun yi Allah wadai
Da take mayar da martani, ƙungiyar gwamnonin Najeriya 36 watau NGF ta yi tir da tashin bam a auyen Zamfara.
Kungiyar, wacce ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici, ta ce harin wani yunkuri ne na ƴan ta'adda matsorata da nufin cutar da ‘yan Najeriya.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke ɗa sa hannun shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq.
A sanarwar da aka rabawa manema labarai ranar Alhamis, kungiyar gwamnonin ta ce:
"Muna kara jaddada goyon bayanmu ga kokarin da sojojin Najeriya ke yi na murkushe wadannan ’yan ta'adda masu aikata miyagun laifuka a ƙasarmu."
Gwamnoni sun jajantawa al'ummar Zamfara
Gwamnonin sun buƙaci mutane su kara sa ido kuma su gaggauta kai rahoton duk wani abin zargin ga hukumomin tsaro domin taimaka masu a yaƙin da suke yi.
NGF ta jajantawa Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara da iyalan wadanda mummunan harin na bam ya shafa.
'Yan sanda sun zargi Lakurawa da kai harin
A wani labarin, an ji cewa rundunar ƴan sandan Zamfara ta zargi ƙunguyar Lakurawa da kai harin bom a Yar Tasha, wanda ya yi sanadin mutuwar matafiya.
Kwamishinan yan sandan jihar shi ne ya bayyana hakan yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng