Sanusi II na Shirin Fita zuwa Bichi, Jami'an Tsaro Sun Mamaye Fadar Sarkin Kano

Sanusi II na Shirin Fita zuwa Bichi, Jami'an Tsaro Sun Mamaye Fadar Sarkin Kano

  • Rahotanni sun bayyana cewa jami'an 'yan sanda da na SSS sun mamaye fadar Sarkin Kano, Kofar Kudu a yau Juma’a
  • An hana mutane shiga da fita daga fadar yayin da ake shirin yi wa Wamban Kano, Munir Sanusi, rakiya zuwa masarautar Bichi
  • Legit ta tattauna da wasu mazauna Kano domin tabbatar da hakikanin abin da yake faruwa a fadar sarkin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Rahotanni daga fadar Sarkin Kano, Kofar Kudu, sun bayyana cewa jami'an tsaro daga rundunar 'yan sanda da kuma SSS sun kewaye fadar da safiyar ranar Juma’a.

An ruwaito cewa matakin jami'an ya kawo cikas ga duk wani motsi na shiga da fita daga fadar Sarkin.

Sarkin Kano
Yan sanda sun mamaye fadar sarkin Kano. Hoto: Abdullahi Dangoggo Koki
Asali: Facebook

Jaridar Daily Nigerian ta wallafa cewa hakan na zuwa ne yayin da mai martaba Muhammadu Sanusi ke shirin fita.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya yi martani yayin da jami'an tsaro suka mamaye fadar sarkin Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin raka Hakimin Bichi zuwa fada

A yau ne sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, zai jagoranci sabon Wamban Kano, Munir Sanusi, zuwa masarautar Bichi bayan nadin da aka yi masa.

Sai dai wannan shiri ya samu cikas sakamakon jibge jami'an tsaro da aka yi a fadar mai martaba Sanusi na II.

Wannan lamari na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun rashin jituwa tsakanin masarautun gargajiya a jihar Kano musamman tsakanin Sanusi II da Aminu Ado Bayero.

Babu shiga babu fita a fadar Kano

Wani mazaninin Kano, Sadisu Sulaiman ya bayyana cewa sun ga jami'an tsaro a fadar wanda suna tunanin akwai siyasa a lamarin.

"Abin da ya ke faruwa, dama yau mai martaba zai raka hakimin Bici sai aka turo ma'aikata suka tare Kofar Kudu, hanyar da zai bi wajen raka hakimin Bichi"

- Isma'il Hamza Abubakar, mazaunin Kano

Wani mai suna Halifa yayi zargin cewa jami'an tsaron sun yi kama da wandanda aka turo daga Abuja domin ba su yi kama da wadanda suka saba gani a Kano ba.

Kara karanta wannan

Yadda Sanusi II ya yi zaman fada duk da jibge jami'an tsaro a gidan Sarkin Kano

An saka jami'an tsaro a masarautar Bichi

A yayin da ake shirin raka sarkin Bichi fadarsa, Daily Nigerian Hausa ta wallafa cewa a can ma an jibge jami'an tsaro.

Ana hasashen cewa hakan zai kawo tsaiko ga duk wani motsi na rakiya ga Hakimin Bichi daga Kano, wanda Muhammadu Sanusi II zai yi a yau.

Moghalu ya ziyarci Sanusi II a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya gana da wani abokinsa da da suka yi aiki tare a bankin CBN.

Bayan dawowarsa daga Amurka, Farfesa Kingsley Moghalu ya ziyarci sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a fadarsa a wata ziyara ta ban girma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng