EFCC Ta Yi Bayanin 'Samun' N700bn a Gidan Bello El Rufa'i, Yaron Tsohon Gwamna Ya Nufi Kotu

EFCC Ta Yi Bayanin 'Samun' N700bn a Gidan Bello El Rufa'i, Yaron Tsohon Gwamna Ya Nufi Kotu

  • Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC), ta yi bayani game da kai samame gidan Bello El Rufa'i
  • An samu wasu rahotanni da ke nuna cewa jami'an EFCC sun kama tsabar kudi har N70b a gidan dan majalisar da ke Kaduna
  • Amma a martanin da hukumar EFCC ta yi, ta bukaci jama'a su yi watsi da rahotannin da ake yada wa na kai samamen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC), ta fito da bayanai a kan kai samame gidan dan tsohon gwamnan Kaduna, Bello El Rufa'i.

Bayanin EFCC na zuwa ne bayan Bello El Rufa'i ya yi barazanar daukar matakin shari'a a kan masu yada labarin cewa an kai samame gidansa.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Barau ya bukaci majalisa ta mayar da sunan Yusuf Maitama a jami'ar FUE

Hukum
EFCC ta musanta kai samame gidan Bello El Rufa'i Hoto: @Oummiih/Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Twitter

A martanin da EFCC ta yi a shafinta na Facebook, hukumar ta ce ta ce babu kamshin gaskiya a labarin cewa jami'anta sun dura gidan Bello El Rufa'i.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar EFCC ta yi bayanin 'samamen' gidan El Rufa'i

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa hukumar EFCC ta karyata cewa an kama tsabar kudi, N700bn da miyagun kwayoyi a gidan dan majalisar Kaduna.

Wannan na zuwa bayan an samu rahotannin cewa jami'an EFCC sun yi nasarar kai mamaya gidan dan majalisa mai wakiltar Kaduna ta Arewa.

EFCC ta musanta zancen kame a gidan Bello El-Rufa'i

Hukumar EFCC ta shawarci jama'a su yi watsi da labarin da ke cewa ta gano miyagun kwayoyi da makudan kudi a gidan dan majalisa.

Hukumar ta ce jami'anta ba su kai ziyara gidan Bello El Rufa'i a Kaduna ba, kuma labarin da ake yada wa karya kawai aka shirya a kan ayyukan da EFCC ta ke yi.

Kara karanta wannan

An samu budurwa mai shekaru 19 tsirara bayan kubuta daga hannun masu tsafi

El-Rufa'i ya karyata kai samame gidansa

A wani labarin, mun ruwaito cewa dan majalisa mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Bello El Rufa'i ya fusata da samun labarin cewa jami'an EFCC sun kai same gidansa a Kaduna.

Hon. Bello El Rufa'i ya bayyana labarin da cewa tsagwaron karya ne, kuma an yi haka ne domin a bata masa suna, lamarin da ya ce zai dangana da matakin shari'a don kwato hakkinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.