Mata Ta Jawo Kotu Ta Tasa Keyar Dan Takarar Gwamna da Mutane 3 Gidan Kaso, Ta Jero Dalilai
- Wata kotun majistare a jihar Edo ta daure wani dan siyasa mai suna Paul Okungbowa kan zargin bata suna da cin zarafi
- Kotun ta daure Okungbowa wanda ya yi takara a zaɓen gwamnan Edo da aka gudanar a 2024 karkashin jam'iyyar YPP
- Ana zargin Okungbowa da kiran wata mata da karuwa a gaban mijinta wanda kotun ke ganin hakan zai jawo husuma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Kotu ta daure dan takarar gwamna na jam’iyyar YPP a zaben gwamnan jihar Edo a 2024, Paul Okungbowa.
Kotun majistare ta daure dan siyasar har tsawon watanni shida a gidan yari kan zargin bata suna.
An daure dan takarar gwamna a gidan kaso
Ana zargin Okungbowa da laifin sakaci da kuma bata suna bayan ya zargi wata uwa da ke da 'ya 'ya a makarantarsa da karuwanci, cewar PM News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Okungbowa wanda shi ne mai makarantar Calvary Crown Academy da ke birnin Benin, an yanke masa hukunci tare da wasu malamai uku.
Daga cikin malaman da aka yanke musu hukuncin sun hada da Blessing Osarodion da Egharevba Esosa da kuma Isioma Nimen.
Alkalin kotun Caroline Oghuma ce ta jagoranci shari’ar, ta ba wadanda ake tuhuma zabin biyan tara maimakon ɗaurin gidan yari.
Abin da ake zargin Okungbowa ya fadawa matar
A cewar takardar karar, an zargi Okungbowa da zagin Blessing Aigbudu, wata uwa da ke da yara biyu a makarantarsa, a ranar 8 ga Satumbar 2023.
An bayyana cewa ya kira matar da karuwa a gaban mijinta da wasu mutane abin da aka ce ka iya haifar da tashin hankali.
Wannan hukunci ya jawo ce-ce-ku-ce a jihar, musamman duba da cewa Okungbowa ya nemi kujerar gwamna a jihar.
'Dan takarar gwamna ya fice daga jam'iyyar LP
Kun ji cewa yayin da LP ke shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2027, tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Edo ya fice daga jam'iyyar.
Kenneth Imansuangbon ya tabbatar da barin LP a wata wasiƙa da ya aikewa shugaban jam'iyyar na ƙasa, Julius Abure a makon nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng