Kudirin Haraji Ya Kawo Sabani a Majalisa, Barau da Akpabio Sun Saba
- Sanata Opeyemi Bamidele ya musanta rahotannin da ke cewa an dakatar da tattaunawa kan ƙudirin gyaran haraji
- Ya bayyana cewa majalisar Dattawa ta kafa kwamiti ne don tattaunawa kan muhimman matsaloli da suka shafi ƙudirin
- Haka zalika, shugaban majalisar Sanata Godswill Akpabio ya tabbatar da ci gaba da ayyukan majalisa kan ƙudirin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta ta musanta rahotannin cewa an dakatar da tattaunawa kan ƙudirin haraji.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele ya musanta rahotannin wasu kafafen yada labarai da ke cewa an janye ko dakatar da ƙudirin.
Vanguard ta wallafa cewa Sanatan ya ce majalisar ta ci gaba da tattaunawa domin samo mafita kan batutuwan da ke da matsala.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin zaman majalisar na yau Alhamis, Bamidele ya ce an kafa kwamitin musamman ne domin aiki tare da Antoni Janar na kasa, Lateef Fagbemi wajen warware matsalolin ƙudirin.
Majalisa ta dakatar da kudirin haraji?
Sanata Bamidele ya yi tir da rahotannin da ke cewa an dakatar da aiki kan ƙudirin, yana mai cewa wadannan rahotanni ba su dace ba kuma suna nufin kawo cikas ga ayyukan majalisa.
"Ba mu dakatar da tattaunawa kan ƙudirin gyaran haraji ba. Yunkurin tsoratar da majalisa ya saba wa tsarin dimokuraɗiyya.
"Majalisa tana da 'yanci da karfin ikon gudanar da ayyukanta bisa kundin tsarin mulki."
- Sanata Opeyemi Bamidele
Kalaman Barau da Akpabio sun saba
A zaman majalisar na ranar Laraba Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa an dakatar da ayyukan majalisa kan ƙudirin har sai an yi shawara da Antoni Janar na Tarayya.
Sanata Jibrin ya umurci kwamitin majalisar kan kudi da ya dakatar da shirin sauraron jama’a da sauran ayyuka har sai an warware matsalolin.
A daya bangaren, Daily Trust ta wallafa cewa shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa majalisar ba ta dakatar da ayyukanta kan ƙudirin ba.
Abejide ya yi magana kan kudirin haraji
A wani rahoton, kun ji cewa dan majalisar tarayya, Leke Abejide ya ce an saka siyasa da addini a kan tattaunawa da ake a kan kudirin haraji.
Hon. Leke Abejide ya ce a dalilin haka ne aka samu wasu na cewa akwai shirin karbar haraji a cikin kudin rabon gadon a kudirin.
Asali: Legit.ng