Yan Sanda Sun Cafke Ma'aikacin Bankin da Ya Sace N18m Na Wani Abokin Hulda
- Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta yi caraf da wani ma'aikacin banki bisa zarginsa da satar kuɗaɗe
- Jami'an ƴan sandan sun cafke wanda ake zargin ne bayan wani kwastoma ya shigar da ƙorafi kan satar da aka yi masa a asusun ajiyarsa
- Ƴan sandan sun bayyana cewa wanda ake zargin ya haɗa baki da wani abokin aikinsa wajen satar ta N18m
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta cafke wani ma'aikacin banki bisa zargin yin sata.
Rundunar ƴan sandan ta cafke ma'aikacin bankin ne a garin Daura, bisa zarginsa da satar Naira miliyan 18 daga hannun wani kwastoma ta hanyar ATM.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar da kamen a lokacin da yake ganawa da manema labarai a hedkwatar ƴan sanda da ke Katsina, cewar rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma'aikacin banki ya shiga hannun ƴan sanda
Wanda ake zargin, mataimakin jami’in ayyuka a wani banki, ana zarginsa da haɗa baki da wani abokin aikinsa wajen yin satar.
Kamen dai ya biyo bayan ƙorafin da wanda aka yi wa satar, Okojie Herbert, ya shigar ne a gaban ƴan sanda.
"Wanda ake zargin ya haɗa baki da wani abokin aikinsa, David Mesioye, wanda a yanzu haka ya tsere, suka sace kuɗi N18,164,000.00 daga asusun bankin wani kwastoma."
"An ci gaba da gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa aikata laifin da ake tuhumarsa da shi."
"An ƙwato kuɗi N10,180,000.00 daga asusun ajiyarsa na banki daban-daban, tsabar kuɗi N366,900 da sauran wasu abubuwan."
"Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike."
- ASP Abubakar Sadiq Aliyu
Ƴan sanda sun gano wajen ƙera bindigu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sanda a jihar Akwa Ibom sun gano wani wuri inda ake ƙera bindigu da saurin makamai.
Jami'an ƴan sandan sun cafke wani daga cikin mutanen da ake zargi suna ƙera makaman a masana'antar wacce ta wani mutum ce da ƴaƴansa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng