LP Ta Yi Magana bayan 'Yan Majalisarta Sun Fice daga Jam'iyya, Za a Dauki Mataki

LP Ta Yi Magana bayan 'Yan Majalisarta Sun Fice daga Jam'iyya, Za a Dauki Mataki

  • LP ta hasala bayan ficewar wasu daga cikin 'yan majalisarta kwanaki kadan da barin tsohon dan takararta daga jam'iyya
  • Jami'in hulda da jama'a na LP, Obioro Ifoh ne ya bayyana takaicin da jam'iyyar ta shiga, kuma ya ce za a dauki mataki
  • Wasu daga cikin matakan da ake shirin dauka ya hada da kunyata su da neman a sauke dukkaninsu daga kujerun da su ke kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Jam’iyyar LP ta yi tir da sauya shekar wasu dan majalisunta a majalisar wakilai zuwa jam’iyyar APC.

Jami'in hulda da jama'a na jam’iyyar, LP na kasa, Obiora Ifoh, ne ya bayyana haka a Abuja a ranar Alhamis, inda ya kara da cewa sam ba su san siyasa ba.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare, gwamnatin Tinubu ta kori ma'aikata masu 'digiri dan kwatano'

majalisa
LP za ta hukunta 'yan jam'iyyarta da su ka fice Hoto: House of Representatives
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa Mista Ifoh ya sanar da cewa jam’iyyar ta kafa wani wuri da zai bayyana sunayen mutanen da suka bata sunan jam’iyyar domin a kunyata su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar LP za ta hukunta wasu 'yan majalisa

Jam'iyyar LP ta ce nan gaba kadan za ta nemi a sauke 'yan majalisarta da su ka sauya sheka, a kuma ayyana kujerun a matsayin babu wanda ke rike da su.

Ya gargadi 'yan majalisar da su san cewa LP ta na da gwagwadon nata tasirin, kuma sun wulakanta kuri'ar jama'ar da su ka zabe su a inuwarta.

LP ta zargi 'yan majalisunta da abin kunya

LP ta ce 'yan majalisun ta guda hudu da su ka fice daga cikin jam'iyyar sun tafka abin kunya a dimukuradiyya.

Jami'in hulda da jama'a na jam'iyyar, Obioro Ifoh ce Sashe na 68(g) na kundin tsarin mulki na 1999 ya fadi lokacin da dan majalisa zai iya sauya sheka da kuma abin da ya kamata ya faru idan ya bar jam'iyyarsa.

Kara karanta wannan

"Najeriya na bukatar mace ta zama shugaban ƙasa," Babban sarki ya yi bayani

'Yan LP sun koma LP a majalisar wakilai

A baya, mun wallafa cewa, wasu daga cikin 'yan majalisun kasar nan daga LP sun sauya sheka zuwa APC a ranar Alhamis, su ka bayyana cewa sun gamsu da matsayarsu.

Kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ne ya karanta wasikar sauya shekarsu a zaman da aka gudanar, ya nuna wadanda su ka sauya shekar sun fito ne daga jihohi daban-daban.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.