Kudirin Haraji: Majalisar Dattawa Ta Cire Sanata daga Kwamitin da Zai Gana da Minista
- Majalisar dattawa ta cire Sanata Tahir Monguno daga kwamitin da ta kafa wanda zai gana da Antoni Janar kan kudororin sauya fasalin haraji
- A zaman yau Alhamis 5 ga watan Disamba, Majalisar ta maye gurbinsa da Sanata Kaka Shehu mai wakiltar jihar Borno ta Tsakiya
- Majalisar ta ɗauki wannan matakin ne bayan yanke shawarar cire shugabanni a kwamitin mutum 10 da ta kafa don ganawa da Ministan shari'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta yi wani ɗan gyara a kwamitin da ta kafa wanda zai zauna da Antoni-Janar na ƙasa (AGF) kan kudirorin sauya fasalin haraji.
A farkon fara zamanta na yau Alhamis, Majalisar ta cire mai ladabtarwa, Sanata Tahir Monguno (APC, Borno ta Arewa) daga kwamitin.
Majalisa ta maye gurbin Sanata a kwamitin
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa bayan cire Monguno, Majalisar dattawan ta maye gurbinsa da Sanata Kaka Shehu mai wakiltar jihar Borno ta Tsakiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana sa ran kwamitin zai zauna da AGF, Lateef Fagbemi domin warware wuraren da suka jawo tada jijiyoyin wuya a kudirin haraji a yau Alhamis.
A ranar Laraba ne majalisar dattawa ta kafa kwamitin na mutum 10 karkashin jagorancin shugaban marasa rinjaye, Sanata Abba Moro (PDP, Benue ta Kudu), cewar Punch.
Dalilin cire Sanata Monguno daga kwamitin
Sai dai daga baya kuma Majalisa ta yanke shawarar cewa kada manyan jagororinta su shiga kwamitin da zai gana da Antoni Janar, shiyasa ta cire Tahir Mungono.
Shugaban masu rinjaye, Sanata Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti ta tsakiya), ya ce an nada Sanata Abba Moro a matsayin shugaban kwamitin "don tabbatar da gaskiya."
Bayan cimma matsayar cire shugabannin majalisar a zaman yau Alhamis, Sanata Godswill Akpabio ya nemi kaɗa kuri'ar murya, inda dukkan sanatocin suka amince.
Sanata ya nemi a ƙarawa attajirai haraji
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Jimoh Ibrahim ya bai wa gwamnatin tarayya shawarin cewa ta ƙara jigba haraji a kan attajiran ƙasar nan.
Sanatan mai wakiltar jihar Ondo ta Kudu ya ce bai kamata a ƙara matsala ƴan ƙasa da ƙarin haraji ba a daidai lokacin da suka fama da masifar tsadar rayuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng