Hajjin 2023: NAHCON Ta Mayarwa Alhazan Kebbi ₦301.56m saboda Abin da Aka Yi Masu
- NAHCON ta mayarwa alhazan jihar Kebbi da suka sauke farali a 2023 wasu kuɗaɗe a matsayin diyyar haƙkokinsu da aka tauye
- Shugaban hukumar jin daɗin alhazai na Kebbi, Faruku Enabo ne ya bayyana hakan a wani taro da ya gudana a Birnin Kebbi
- Ya ce tuni mai girma gwamna ya ba da umarnin rabawa alhazan kuɗaɗensu, wanda aka fara a kowace ƙaramar hukuma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi - Hukumar Alhazai ta kasa watau NAHCON ta mayarwa Alhazan jihar Kebbi da suka sauke farali a 2023 sama da Naira miliyan 300.
Kowanne mutum daga cikin mahajjata 4,936 da suka yi aikin Hajjin shekarar 2023 za a mayar musu da kudi N61,080.
NAHCON ta mayarwa alhazan Kebbi ₦301.56m
Shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kebbi, Faruku Enabo ne ya bayyana hakan a wurin wani taro da ya jagoranta a Birnin Kebbi, Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce tuni aka saka kudaden a asusun hukumar domin rabawa wadanda suka yi aikin hajjin shekarar 2023.
Ana mayar da waɗannan kudin ne bisa umarnin NAHCON na biyan diyya ga Alhazan sakamakon wasu haƙƙoƙinsu da ba a biya masu a lokacin hajjin 2023 ba.
Kebbi: An fara rabawa alhazai N60,080
Faruku ya ce:
"Bayan na karbi kudin daga hannun hukumar NAHCON, na sanar da gwamna cewa ga kudi an maido, nan take ya umarce ni da fara shirin mayar da kudaden ga maniyyata.
"Dukkan shugabannin kananan hukumomi 21 na jihar Kebbi shaida ne kuma da su ake tsara matakan mayarwa alhazan kuɗinsu."
Jami'an tsaro za su sa ido kan aikin
Faruku Enabo ya bukaci ciyamonin ƙananan hukumomi su sanya ido kan aikin domin tabbatar da cewa dukkan maniyyatan da abin ya shafa sun samu kudinsu.
Ya ƙara da cewa jami'an tsaro za su sa ido da bibiyar aikin don tabbatar da cewa Alhazan sun karɓi kuɗinsu kamar yadda aka tsara.
An biya Alhazan Kano na 2023 diyya
Kun ji cewa hukumar alhazan Kano ta rabawa mahajjatan 2023 na jihar wasu Miliyoyin Naira a matsayin diyyar matasala da aka samu a ƙasa mai tsarki.
Shugaban hukumar ya ce Saudiyya ce ta biya kudin ta hannun hukumar NAHCON sakamakon tangarɗar wutar lamtarki da aka samu yayin aikin hajji.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng