'Yan Sanda Sun Bankado Wurin Kera Bindigogi, Sun Cafke Wadanda Ake Zargi
- Rundunar ƴan sandan jihar Akwa Ibom ta samu nasarar gano wani wuri inda ake ƙera bindigogi da sauran makamai
- Kwamishinan ƴan sandan jihar ya bayyana cewa wurin ƙera makaman na wani mutum ne tare da ƴaƴansa
- CP Joseph O. Oribo ya ce an gano wurin ne bayan an samu sahihan bayanan sirri kan ayyukan da waɗanda ake zargi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Akwa Ibom - Jami’an rundunar ƴan sandan jihar Akwa Ibom, sun gano wata masana’antar ƙera bindigogi.
Ƴan sandan sun gano wurin ne inda wani mutum tare da ƴaƴansa suke ƙera bindigogi iri-iri.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Joseph O. Eribo, ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Ikot Akpan Abia, a birnin Uyo, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan ƴan sandan ya bayyana irin nasarorin da rundunar ta samu wajen yaƙi da miyagun laifuka, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da wannan.
Yadda ƴan sanda suka gano wurin ƙera bindigogi
Joseph Eribo ya bayyana cewa an gano wurin ƙera bindigun ne bayan samun sahihan bayanan sirri.
Ya ce bayan samun bayanan, jami’an ƴan sanda sun garzaya zuwa wajen cikin gaggawa, suka kutsa kai tare da cafke ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi, yayin da sauran suke tsere.
Kayayyakin da aka kwato sun haɗa da sababbin bindigogi guda bakwai da aka ƙera, sababbin bindigogi guda biyar masu ƙofofi biyu da bututun ƙarafunan da ake amfani da su wajen ƙera bindiga.
"A lokacin samamen, an cafke wani mai suna Emmanuel, yayin da mahaifinsa, Akpan Nse Emmanuel, da ƴan uwansa waɗanda ke aikin tare, suka tsere."
- Joseph O. Oribo
Joseph Eribo ya tabbatarwa jama’a cewa ana ci gaba da ƙoƙarin cafke sauran waɗanda ake zargin da suka gudu.
Atiku ya caccaki ƴan sandan Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa, Atiku Abubakar, ya caccaki matakin da ƴan sanda suka ɗauka na cafke mai fafutukar kare hakkin dan Adam a Legas.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya nuna takacinsa kan yadda faɗin albarkacin baki ka sanya ake cafke mutane a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng