Gwamma Ya Gano Kasuwar da Ake Ɓoye Miyagu, Ya Umarci a Rufe Ta Nan Take

Gwamma Ya Gano Kasuwar da Ake Ɓoye Miyagu, Ya Umarci a Rufe Ta Nan Take

  • Gwamnan Kogi, Ahmed Usman Ododo ya ba da umarnin rufe kasuwar Zango saboda taɓarɓarewar tsaro a yankin Osara
  • Kwamishinan yaɗa labarai, Kingsley Fanwo ya ce gwamna ya ɗauki wannan matakin ne bayan gano ana ɓoye ƴan ta'adda a kasuwar
  • Ya ce gwamnatin Kogi ta kuma haramta ajiye manyan motocin a gefen titi, ya ƙara da cewa sun gano ana haɗa baki da direbobi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kogi - Gwamnatin Kogi karkashin jagorancin Gwamna Ahmed Ododo ta bayar da umarnin rufe kasuwar Zango da ke kusa da Osara saboda karuwar matsalar tsaro.

Kwamishinan yada labarai, Kingsley Fanwo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 4 ga watan Disamba, 2024.

Gwamna Ahmed Ododo.
Gwamnatin Kogi ta rufe kasuwar zango saboda barazanar tsaro Hoto: Alhaji Ahmed Usman Ododo
Asali: Twitter

Umurnin da Gwamna Usman Ododo ya bayar ya kuma haramta ajiye motoci a gefen titi a yankin, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

NLC ta janye yajin aiki, gwamna ya amince N80,000 ya zama mafi ƙarancin albashi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya gano ana ɓoye miyagu a kasuwa

Fanwo ya kara da cewa a bayanan sirri da gwamnati ta samu, miyagu na amfani da kasuwar a matsayin mafakarsu tare da taimakon direbobin manyan motoci.

Ya ce gwamnati ta bai wa dukkann ƴan kasuwa da direbobin manyan motocin da ke zama a wurin wa'adin mako guda su tattara su tashi gaba ɗaya.

"Duba da karuwar matsalar tsaro a Osara da kewaye, gwamnatin jihar Kogi ta bayar da umarnin rufe kasuwar Zango cikin gaggawa tare da haramta ajiye motoci a gefen titi. 
"Mun ɗauki wannan matakin ne a wani ɓangare na kokarin magance matsalar tsaron da ta addabi yankin.
"Bayanan sirri sun nuna cewa miyagu na amfani da kasuwar a matsayin maboya, galibi tare da hadin gwiwar wasu direbobin manyan motoci da ke ajiye motoci a bakin titi.

- Kingsley Fanwo.

Matsalar tsaro ta ƙaru a Osara

Kwamishinan ya ce wannan lamari dai ya haifar da babbar barazana ta tsaro ga Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Confluence da ke Osara da sauran al'ummar yankin.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ji kukan ƴar NYSC da malama ta lakadawa duka a Ilorin, ya dauki mataki

Ya ce gwamna ya umarci sakataren gwamnati ya sanar da dukkan waɗanda wannan matakin ya shafa domin tabbatar da kowa ya bi wannan umarni, Punch ta kawo.

Gwamna Ododo ya naɗa karin hadimai

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Ahmed Ododo ya kara yin naɗe-naɗen hadimai da za su taimaka masa wajen sauke nauyin al'umma.

Daga cikin waɗanda gwamnan ya naɗa har da shugaban hukumar kula da makarantun sakandire da ƴan majalisar gudanarwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262