Shugaban Karamar Hukuma Zai Fara Biyan Zawarawa Alawus Duk Wata

Shugaban Karamar Hukuma Zai Fara Biyan Zawarawa Alawus Duk Wata

  • Ciyaman na karamar hukumar Igbo-Ekiti a jihar Enugu, Hon. Eric Odo ya amince ai fara ba zawarawa alawus a kowane wata
  • Mista Odo ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta kula da zawarawa, talakawa da sauran marasa galihu a yankin
  • Shugaban karamar hukumar ya ce amfanin gwamnati shi ne ta inganta rayuwar talaka, don haka zai yi duk mai yiwuwa wajen taimakon al'ummarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Enugu - Shugaban karamar hukumar Igbo-Etiti ta jihar Enugu, Eric Odo, ya amince da fara biyan matan da suka rasa mazajensu alawus duk wata.

Ya ce gwamnatin ƙaramar hukumar tana da karfin tattalin arzikin da za ta zama gatan zawarawa da saura. talakawa saboda halin kuncin da ake ciki.

Jihar Enugu.
Shugaban karamar hukuma a jihar Enugu zai fara biyan zawarawa alawus Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Mista Odo ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin da yake jawabi ga zawarawan yankin Igbo-Etiti da suka kai masa ziyarar ban girma a Ogbede, Premium Times ta kawo.

Kara karanta wannan

An nemi ministan Tinubu ya yi murabus, ya sake neman takarar gwamna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Enugu: Ciyaman zai yi wa zawarawa gata

Ciyaman din ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa ta kare zawarawa daga munanan al'adu da ake yi a kansu.

Ya ce ɗan alawus da za a riƙa ba su duk wata, wanda zai saka a kasafin kudin 2025, zai taimaki matan wajen biyan buƙatun yau da kullum.

Eric Odo ya ƙara da cewa nauyin gwamnati ne ta inganta walwalar talaka kuma ta samar da tsaro da aminci.

Shugaban karamar hukumar ya faɗi manufarsa

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce:

"Ita gwamnati dama dalilin kafa ta kenan, ta inganta rayuwar talakawa ba tare da duba matsayi ko matakin karatunsu ba, kowa talakan gwamnati ne.
"Ina ganin abu ne mai muhimmanci mu fara warware matsalar zawarawa mu taimaki rayuwarsu ta yadda ko bayan mun tafi za a ɗora daga inda muka tsaya.
"Abin da muka zo yi shi ne mu canza halin da ake ciki kuma mu ba kowa kama daga matalauta da marasa galihu damar yin rayuwa mai gamsarwa cikin walwala."

Kara karanta wannan

Atiku ya dura a kan 'yan sanda, ya soki yadda aka kama mai adawa da gwamnati

Ciyaman ya naɗa hadimai 100 a Ribas

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban karamar hukumar Obio-Akpor a jihar Rivers, Chijioke Ihunwo ya naɗa hadimai 100 da za su taimaka masa a ɓangarori daban-daban.

Hon. Chijioke Ihunwo ya ce ya yi waɗannan naɗe-naɗe ne domin aiki tukuru da cika alkawurran da ya ɗaukarwa al'aummarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262