Dan Majalisar Kano Ya Fadi Shirin da Aka Yi Wa Tinubu kan Kudirin Haraji
- Ɗan majalisar wakilai daga jihar Kano, ya fito fili ya nuna adawarsa da ƙudirin haraji da gwamnatin Bola Tinubu ta ɓullo da shi
- Hon. Ghali Mustapha mai wakiltar Albasu/Gaya/Ajingi ya caccaki ƙudirin wanda ya bayyana a matsayin mara amfana ga talaka
- Ɗan majalisar da ke mulki a inuwar NNPP ya yi nuni da cewa za su yi bakin ƙoƙarinsu domin ganin cewa ƙudirin bai zama doka ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ɗan majalisar wakilai daga jihar Kano, Ghali Mustapha, ya caccaki kuɗirin harajin da aka fito da shi..
Hon. Ghali Mustapha ya bayyana cewa ƙudirin sake fasalin haraji ba shi da amfani ga talaka.
Ɗan majalisar na jam'iyyar NNPP mai wakiltar Albasu/Gaya/Ajingi ya bayyana hakan ne lokacin da yake da magana da manema labarai a Abuja, cewar rahoton jaridar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ghali Mustapha ya caccaki ƙudirin harajin Tinubu
Ya ce ƙudirin zai ƙara taɓarɓarar da halin matsin tattalin arziƙin da ake fama da shi a ƙasar nan, idan har aka amince ya zama doka.
Ɗan majalisar ya ce shi da takwarorinsa za su yi iya bakin ƙoƙarinsu domin hana amincewa da ƙudirin.
"A halin da ake ciki yanzu, manufofin wannan gwamnati mai ci sun yi tsauri, kuma suna wahalar da talaka."
"Ina ganin kuskure ne su kawo wannan batu na yin muhawara kan sake fasalin haraji."
"Ba mu san wanda ke bayan wannan ƙudirin harajin ba. Mun san ɓangaren zartaswa ya dage wajen ganin an zartar da ƙudirin. Amma za mu yi iya ƙoƙarinmu don dakatar da wannan ƙudirin."
"Kuma ina tabbatar muku da cewa mafiya yawan ƴan majalisar da na zanta da su ba su damu da wannan ƙudirin ba, domin abin da ya fi muhimmanci a yanzu shi ne yadda za a samarwa talakawa abinci."
- Ghali Mustapha
Sheikh Gumi ya goyi bayan ƙudirin haraji
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmed Gumi, ya tofa albarkacin bakinsa kan ƙudirin haraji da gwamnatin Bola Tinubu ta kawo.
Sheikh Ahmed Gumi ya nuna goyon bayansa ga ƙudirin, yana mai cewa dokokin suna da amfani sosai ga ƴan Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng