Rundunar Sojoji Ta Cafke Jami'anta saboda Cin Zarafin Farar Hula

Rundunar Sojoji Ta Cafke Jami'anta saboda Cin Zarafin Farar Hula

  • Wasu jami'an soja sun debo ruwan dafa kansu bayan an gansu a bidiyo su na cin zarafin fararen hula biyu a Legas
  • Lamarin ya dagawa jama'a hankali, inda da yawa daga cikinsu su ka fusata, lamarin da ya sa rundunar fitar da sanarwa
  • Rundunar sojojin ta dauki alkawarin kara zurfafa bincike, tare da hukunta sojojin wanda tuni aka gano su waye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Wasu jami'an rundunar sojin kasar nan sun fusata shugabanninsu bayan an gano su na cin zarafin wani farar hula a Legas.

Nigerian
Sojoji sun kama jami'anta 2 Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Wannan na zuwa ne bayan an dauki sojojin a bidiyo, inda aka rika ganin yadda sojojin su ka ci zarafin farar hula guda biyu a Badagry, Legas.

Kara karanta wannan

Atiku ya dura a kan 'yan sanda, ya soki yadda aka kama mai adawa da gwamnati

TVC News ta ruwaito cewa rundunar ta bayar da hakuri ga jama'ar da lamarin ya fusata, ta kara da cewa bincike ya yi nisa domin gano musabbabin abin da ya faru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun fara binciken jami'ansu

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa rundunar sojojin kasar nan ta fitar da sanarwa game da cin zarafin wasu mutane biyu a Legas.

Rundunar ta bayyana cewa tuni aka gudanar da kwarya-kwaryan bincike a kan lamarin da ya harzuka jama'a, kuma za a dauki mataki.

“Ana gudanar da cikakken bincike ta hannun kan wadanda ake zargi. Muna ttabbatar maku da cewa za a tabbatar da adalci yadda ya kamata.”

Za a ladabtar da sojojin ƙasa

Rundunar sojojin kasar nan ta bayar da tabbacin hukunta jami'anta da aka gani su na cin zarafin wasu mutane da Badagry.

Jama'a sun rika tofa albarkacin bakinsu, tare da nuna fushi a kan yadda jami'an su ka ci zarafin mutanen bayan sabanin da ya shiga tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Barau ya bukaci majalisa ta mayar da sunan Yusuf Maitama a jami'ar FUE

Sojoji sun kai harin bama bamai

A baya, mun ruwaito cewa sojojin kasar nan sun kai harin bama-bama Zamfara, su ka durfafi sansanonin miyagun 'yan ta'adda da ke kai hare-haren kan jama'a.

Daga sansanonin da aka kai wa hari, har da na kasungurmin dan ta'adda, Ado Aliero, aka yi nasarar shafe da yawa daga cikin 'yan ta'adda a hare-haren da aka kai wurare da dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.