Yadda Gobara Ta Lalata Kayayyakin Miliyoyin Naira a Jihar Kano
- Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta yi bayani kan ayyukan da ta gudanar a cikin watan da ya gabata na Nuwamba
- Kakakin hukumar kashe gobarar, ya ce an samu asara ta kayayyakin da darajarsu ta kai ta N132,450,000 a watan na Nuwamba
- Saminu Abdullahi ya kuma bayyana cewa sun samu nasarar ceto rayukan mutane huɗu da gobara ta ritsa da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana cewa gobara ta lalata kayayyakin da suka N132,450,000, a faɗin jihar a watan Nuwamban 2024.
Hukumar kashe gobarar ta kuma tabbatar da mutuwar mutane uku, tare da ceto wasu mutane huɗu a yayin ayyukanta a watan da ya gabata.
Hukumar kashe gobara ta yi ƙoƙari a Kano
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta Kano, Saminu Abdullahi ya fitar, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar ta bayyana cewa sun amsa kiran kai ɗauki guda 43, sun samu kiran ƙarya guda shida, sun yi ayyukan ceto biyar a ofisoshinsu guda 29 da ke faɗin jihar.
Duk da asarar da aka samu, hukumar kashe gobarar ta ceto kayayyakin da darajarsu ta kai N310,600,000 daga lalacewa ta hanyar ɗaukar matakan gaggawa.
Hukumar ta ceto dukiyoyi daga gobara
Saminu Abdullahi ya koka da asarar rayuka da dukiyoyi amma ya yaba da ƙoƙarin da jami’an hukumar ta kashe gobara suka yi.
"Mun yi baƙin cikin sanar da cewa an yi asarar rayuka uku a tashin gobarar, amma tawagarmu ta yi nasarar ceto mutane huɗu tare da ceto kayayyakin da darajarsu ta kai sama da Naira miliyan 310."
- Saminu Abdullahi
Gobara ta laƙume kayayyaki a Kwara
A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin wata gobara a kasuwar Ita Amodu da ke kan tsohon titin Yidi a birnin Ilorin na jihar Kwara, inda ta lalata kayayyaki masu yawa.
Gobarar da ta auku dai, ta takaita mazauna yankin da ’yan kasuwa da ke sayar da katifu, dadduma da sauran kayayyaki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng