"Ba Talakawa Ya Kamata a Tatsa Haraji ba," Sanata Ibrahim Ya Kawo Mafita

"Ba Talakawa Ya Kamata a Tatsa Haraji ba," Sanata Ibrahim Ya Kawo Mafita

  • Sanatan Ondo ta Kudu, Jimoh Ibrahim ya ce attajiran Najeriya ba su biyan harajin da ya kamata duk da ƙoƙarin da gwamnati take masu
  • Jimoh Ibrahim ya kuma shawarci gwamnatin tarayya da jihohi su rika taimakawa talakawa da abinci duk wata
  • A cewarsa, ta wannan hanya ne kaɗai za a sauke farashin kayan amfani da yau da kullum da kuma rage wahalhalun da ake ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Sanata Jimoh Ibrahim ya zargi masu hannu da shuni a Najeriya da rashin biyan kudaden haraji ga gwamnati yadda ya kamata.

Sanatan mai wakiltar jihar Ondo ta Kudu ya bayyana haka ne da yake jawabi a zaman majalisar dattawa na jiya Talata, 3 ga watan Disamba, 2024.

Sanata Jimoh Ibrahim.
Sanata Jimoh Ibrahim ya koka cewa attajirai ba su biyan harajin da ya kamata a Najeriya Hoto: Senator Jimoh Ibrahim
Asali: Twitter

Ya ce duk da attajiran Najeriya na samarwa mutane ayyukan yi, ya kamata su riƙa biyan harajin kadarorinsu na alfarma, kamar yadda The Nation ta kawo.

Kara karanta wannan

Shugaban karamar hukuma zai fara biyan zawarawa alawus duk wata a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haraji: Sanata Jimoh Ibrahim ya kawo mafita

Da yake jawabi ga masu ɗauko rahoto a majalisar tarayya, Sanata Jimoh Ibrahim ya ce:

"Ya kamata masu kudi su biya haraji fiye da sauran mutane, na san za su iya biya. Mun san suna samar da ayyukan yi to amma akwai buƙatar su biya harajin kadarorinsu na alfarma."

Jimoh Ibrahim ya ce gwamnati tana taimakawa kasuwancin attajirai ta hanyoyi da dama, don haka ya kamata su ɗauki biyan haraji da muhimmanci.

"Ba ina nufin mu kara matsalawa talakawa da ƙarin haraji ba, amma a wannan mawuyacin halin da muke ciki, ya kamata attajirai su kara yawan harajin da suke biya," in ji shi.

Yadda gwamnati za ta rage tsadar rayuwa

Ibrahim ya kuma ba da shawarin cewa ya kamata gwamnatin tarayya da jihohi su riƙa rabawa talakawa miliyan 30 tallafin baucar abinci ta N100,000 duk wata.

Sanatan na Ondo ta Kudu ya ce hakan zai rage illar tsadar kayayyaki da kuma wahalhalun da ke tattare da ita a kasar nan, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Najeriya na bukatar mace ta zama shugaban ƙasa," Babban sarki ya yi bayani

Akpabio ya yi barazana a majalisa

A wani rahoton, an ji cewa shugaban majalisar dattawa ya yi barazanar tsige duk shugaban kwamitin da ya yi sakaci da aikin da ke kansa.

Sanata Godswill Akpabio ya ce majalisar dattawa ba za ta lamurci gazawar waɗanda ta aminta da su, ta ba su amana ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262