NLC: Gwamna Ya Fara Biyan Sabon Albashin N80,000, Ma'aikata Sun Gano Matsala
- Gwamnatin jihar Enugu karkashin jagorancin Gwamna Peter Mbah ta fara biyan sabon albashi mafi kankanta na N80,000 tun a Nuwamba
- Ƙungiyoyin ma'aikata na jihar da suka haɗa da NLC da TUC ne suka tabbatar da haka a wata sanarwar haɗin guiwa ranar Talata
- Sun ce an samu wani ɗan tuntuɓe wajen aiwatar da ƙarin albashin amma sun sanar da gwamnan kuma suna ganin zai ɗauki mataki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Enugu - Kungiyoyin kwadago a Enugu sun musanta zargin da ake cewa har yanzu ba a fara biyan sabon mafi karancin albashi a jihar ba.
Ƴan kwadagon sun bayyana cewa tun a karshen watan Nuwambar 2024 ma'aikata suka fara karɓan sabon albashi na N80,000 da gwamna ya amince.
Hakan na kunshe a wata sanarwar haɗin guiwa mai ɗauke da sa hannun shugaban NLC, Fabian Nwigbo, na TUC, Ben Asogwa da shugaban kwamitin tattaunawa, Ezekiel Omeh.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A rahoton Daily Trust, sanarwar ta ce kamar yadda Gwamna Peter Mbah ya yi alƙawari, gwamnatinsa ta fara biyan mafi ƙarancin albashi N80,000 a watan Nuwamba.
Gwamna Mbah ya fara biyan albashin akalla N80,000
Wani sashen sanarwar ya ce:
"Muna tabbatar da cewa gwamnatin jihar Enugu ta biya mafi karancin albashi na N80,000 da gwamna ya amince da shi a cikin albashin watan Nuwamba na 2024."
Sai dai ƴan kwadagon sun nuna damuwa kan rashin aiwatar da tsare-tsaren ƙarin albashin ma'aikata da ke kunshe a dokar sabon mafi ƙarancin albashin ba.
Ƴan kwadago sun aika saƙo ga gwamnan Enugu
Shugabannin kungiyoyin kwadagon sun tabbatar da cewa tuni suka sanar da mai girma gwamna matsalolin da aka samu kuma suna da yaƙinin zai yi wani abu a kai.
A rahoton PM News, ƴan kwadagon suka ce:
"Amintarmu da ƙwarin guiwar da muke da ita a kan mai girma gwamna ba ta sauya ba, duba da yadda ya ɗauki walwalar ma'aikata da nuhimmanci."
"Gwamna ya ci gaba da biyan tallafin albashi na N25,000 ga ma’aikata tun daga Disamba 2023 har zuwa Oktoba 2024 lokacin da aka amince da sabon albashi na N80,000."
Kungiyar NLC ta janye yajin aiki a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa ma'aikatan gwamnati a jihar Kaduna sun janye yajin aikin da suka fara saboda sabon mafi karancin albashi.
Shugaban NLC reshen jihar Kaduna, Ayuba Sulaiman ya godewa ma'aikata bisa biyayya ga umarnin kungiya, ya tabbatar masu da cewa kowa zai samu ƙarin albashi da ya dace.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng