Gobara Ta Tashi a Ofishin Hukumar INEC, Ta Yi Barna Mai Girma

Gobara Ta Tashi a Ofishin Hukumar INEC, Ta Yi Barna Mai Girma

  • An samu tashin gobara a ofishin hukumar zaɓe ta INEC a jihar Delta da ke yankin Kudu maso Kudu na Najeriya
  • Gobarar da ta tashi a ranar Litinin dinnan ta yi ɓarnata kayayyaki masu yawa na hukumar zaɓen ta INEC
  • Hukumar zaɓen ta bayyana cewa ba a samu waɗanda suka jikkata ba, ko rasa ransu a sakamakon tashin gobarar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ta tabbatar da aukuwar gobara a ofishinta da ke ƙaramar hukumar Ika ta Arewa maso Gabas, a jihar Delta.

Gobarar wacce ta tashi a ofishin na hukumar INEC ta lalata kayayyyaki masu yawa.

Gobara ta tashi a ofishin INEC a Delta
Gobara ta yi barna a ofishin INEC a Delta Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Tabbatar da aukuwar gobarar ne ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na INEC, Sam Olumekun, ya fitar a shafin X na hukumar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki gwamna a Najeriya, gwamnati ta yi bayani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gobara ta yi ɓarna a ofishin hukumar INEC

Jami'in ya bayyana cewa gobarar ta lalata kusan akwatunan zaɓe 706, jakunkunan zaɓe 50, riguna 322, da sauran kayayyaki.

A cewar sanarwar, kwamishinan zaɓe (REC) na jihar Delta, Mista Etekamba Udo Umoren, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wani rahoto.

Rahoton ya bayyana cewa lamarin ya auku ne da yammacin ranar Litinin, sakamakon tartashin wutar lantarki.

"Ɓangaren ajiya inda ake ajiye janaretoci da sauran kayayyaki ya ƙone ƙurmus."
"Kayayyakin da gobarar ta lalata sun haɗa da akwatunan zaɓe 706, jakunkunan zaɓe 50, riguna 322, janaretoci guda uku, tambari 140, hatimin akwatin zaɓe 50 da sauransu."
"Cikin sa’a, ba a samu raunuka ko asarar rayuka ba. Tuni dai aka kai rahoton faruwar lamarin ga hukumomin tsaro da masu ba da agajin gaggawa domin gudanar da cikakken bincike."

- Sam Olumekun

Gobara ta tashi a kasuwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata gobara da ta tashi a kasuwar Ita Amodu da ke kan tsohon titin Yidi a birnin Ilorin na jihar Kwara, ta lalata kayayyakin miliyoyin Naira.

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta laƙume kayan miliyoyin Naira a babban birnin jihar Kwara

Gobarar da ta auku a ranar Talata, 3 ga watan Disamba, ta takaita mazauna yankin da ƴan kasuwa da ke sayar da katifu, dadduma da sauran kayayyaki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng