Dakarun Sojojin Sun Saki Bama Bamai a Sansanin 'Yan Ta'adda, An Hallaka Miyagu Masu Yawa
- Dakarun sojojin saman Najeriya sun kai hare-hare kan sansanonin ƴan ta'adda a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma
- Sojojin sun hallaka ƴan ta'adda masu yawa bayan sun saki bama-bamai a sansanoninsu da ke ƙaramar hukumar Tsafe
- Daga cikin sansanonin da aka kai hare-haren har da na riƙaƙƙen shugaban ƴan ta'adda, Ado Aliero
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Dakarun sojojin sama Najeriya na rundunar Operation Fansan Yamma, sun ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin ƴan ta'adda a jihar Zamfara.
Daga cikin wuraren da dakarun sojojin suka kai harin har da sansanin fitaccen shugaban ƴan ta’adda, Ado Aliero.

Source: Getty Images
Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
Sojojin sama sun saki bama-bamai kan ƴan ta'adda
Daga cikin wuraren da aka farmaka har da gidan wani fitaccen ɗan ta’adda mai suna Dan Umaru da ke garin Madeli, kusa da Yan Kuzu a yankin Arewa maso Yammacin ƙaramar hukumar Tsafe.
Hare-haren ta sama, wanda aka kai, an kai su ne da nufin tarwatsa maɓoyar ƴan ta'addan da kuma daƙile ayyukansu a yankin.
Bayanan sirri sun bayyana waɗannan wuraren a matsayin yankunan tsarawa da ƙaddamar da hare-hare kan ƙauyuka.
Sojoji sun hallaka miyagun ƴan ta'adda
Shaidun gani da ido da ke yankin sun bayyana cewa bama-baman sun lalata gine-gine da ke cikin sansanonin, lamarin da ya janyo hallaka ƴan ta'adda masu yawa.
Majiyoyi sun bayyana cewa, hare-haren sun kawar da ƴan ta'adda masu yawa.
"A halin yanzu muna ganin wuta na ci a gidan Dan Umaru. An kashe da dama daga cikinsu."
- Wata majiya
Dakarun sojoji sun sheƙe ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai, sun samu nasarar hallaka ƴan ta'addan Boko Haram.
Sojojin tare da haɗin gwiwar ƴan sa-kai na CJTF sun samu nasarar hallaka ƴan ta'addan guda biyar a ƙaramar hukumar Mafa ta jihar Borno.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
