Afrika ta Kudu: Ramaphosa Ya Fadi Ta Fuskar da Ya ke Fatan Karfafa Alaka da Najeriya

Afrika ta Kudu: Ramaphosa Ya Fadi Ta Fuskar da Ya ke Fatan Karfafa Alaka da Najeriya

  • Afrika ta Kudu ta bayyana fatan kara dankon alaka da kasar nan ta fuskoki da dama don cigaban kasashen biyu
  • Shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa ne ya shaidawa shugaban kasar nan, Bola Ahmed Tinubu haka a ranar Talata
  • Ya yi fadi matakan da ya dauka wajen rage kalubalen shiga yankin domin gudanar da kasuwanci da yawon bude ido

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar South Africa - Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya bayyana bangarorin da ya ke fatan alakar Najeriya da kasarsa ta kara danko.

Cyril Ramaphosa ya tallatawa Tinubu da sauran masu abin hannu a Najeriya kasarsa, ya ce ta na daga cikin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika.

Kara karanta wannan

Tinubu ya saurari kukan jama'a kan ƙudirin haraji, ya ba da sabon umarni

Tinubu
Afrika ta Kudu na son karfafa alaka da Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa shugaban Afrika ta Kudu ya ce su na maraba da duk wani da ke sha'awar zuba hannun jari a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ya yi alkawarin kasarsa za ta yi abin da ya dace wajen karfafa tattalin arzikin manyan kasashen biyu.

An bude kofar Afrika ta Kudu ga Najeriya

Jaridar PM News ta wallafa cewa kasar Afrika ta Kudu ta saukaka wa 'yan Najeriya samun takardar shiga kasar ga masu yawon bude idanu da 'yan kasuwa.

Shugaban kasar ne ya sanar da shugaban Najeriya, Bola Tinubu haka, jim kadan bayan bude taron tattaunawa tsakain Afrika ta Kudu na Najeriya karo na 11.

Shirin Afrika ta Kudu kan Najeriya

Shugaba Cyril Ramaphosa ya ce kasar za ta rubanya kokarinta wajen cire kalubalen da ke kawo cikas tsakanin kasashen biyu, musamman ta fuskar cinikayya.

Ya yaba da tsare-tsaren da gwamnatin Najeriya ke yi don a kokarinta na ba sauran kasashen duniya kwarin gwiwar zuba hannun jari a kasarsa don habaka tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 10 da Tinubu ya fada yayin jawabinsa a kasar Afrika ta Kudu

Tinubu ya sauka a Afrika ta Kudu

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasar nan, Bola Ahmed Tinubu ya fice zuwa Afrika ta Kudu a lokacin da muhawar ta yi zafi kan batun kudirin haraji ya ke son a zartarwa a Najeriya.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu da tawagarsa sun sauka Cape Town na kasar Afrika ta Kudu a daren ranar Litinin domin halartar taron kungiyar kasar Najeriya da Afirka ta Kudu karo na 11.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.