'Yan Bindiga Sun Farmaki Gwamna a Najeriya? Gwamnati Ta Yi Bayani

'Yan Bindiga Sun Farmaki Gwamna a Najeriya? Gwamnati Ta Yi Bayani

  • An yaɗa wasu rahotanni masu cewa ƴan bindiga sun farmaki ayarin motocin Gwamna Mohammed Umaru Bago na Neja
  • Gwamnatin jihar ta fito ta yi martani inda ta musanta waɗannan rahotannin da aka yi ta yaɗawa a wasu kafafen yaɗa labarai
  • Ta bayyana cewa babu wani batun barazana ga lafiyar Gwamna Bago ko ƴan tawagarsa da suke yin rangadi tare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Gwamnatin jihar Neja ta yi martani kan rahotannin da ake yaɗawa cewa wasu ƴan bindiga sun farmaki tawagar Gwamna Umaru Bago.

Gwamnatin Neja ta ƙaryata rahotannin waɗanda aka yaɗa a wasu kafafen watsa labarai, kan cewa ƴan bindiga sun farmaki ayarin motocin gwamnan a ƙaramar hukumar Mashegu ta jihar.

'Yan bindiga ba su farmaki Gwamna Bago ba
Gwamnatin Neja ta musanta cewa 'yan bindiga sun farmaki ayarin Gwamna Umaru Bago Hoto: @HonBago
Asali: Facebook

Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar, Bologi Ibrahim, ya fitar, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon shugaban NLC ya mutu bayan ƴar hatsaniya da ƴan sanda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me gwamnati ta ce kai wa Gwamna Bago hari?

Jami'in ya bayyana labarin a matsayin maras tushe ballantana makama wanda babu ƙamshin gaskiya a cikinsa.

Bologi Ibrahim ya yi nuni da cewa ayarin motocin gwamnan na ci gaba da rangadin ayyukan da ake gudanarwa a yankin Neja ta Arewa, cikin kwanciyar hankali tun daga makon da ya gabata.

"Ziyarar Gwamnan ta kasance cikin lumana ba tare da wani hari ko barazana ga lafiyarsa ko ta tawagarsa ba."
"Rangadin gwamnan na tafiya cikin lumana ba tare da wani batun hari ko barazana ga lafiyarsa ko ta ƴan tawagarsa ba."
"Gwmana Umaru Bago yana samun tarba mai kyau daga mutanen dukkanin wuraren da ya ziyarta ya zuwa yanzu."

- Bologi Ibrahim

Bologi Ibrahim ya ƙara da cewa jami'an tsaro tare da haɗin gwiwar masu samar da tsaro a yankunan, suna bakin ƙoƙarinsu wajen tabbatar da tsaron lafiyar dukkanin mutanen da ake yin rangadin da su.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon ɗan Majalisar Tarayya, sun kashe ɗan sanda

Ƴan bindiga sun sace tsohon ɗan majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun yi garkuwa da tsohon ɗan majalisar wakilan tarayya, Hon. Dr. Joseph Haruna Kigbu a hanyar zuwa Jos.

Maharan sun sace tsohon ɗan majalisar a tsakanin kauyen Nunku a ƙaramar hukumar Akwanga da ke Nasarawa da Gwantu a yankin Sanga a Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng