Mummunar Gobara Ta Laƙume Kayan Miliyoyin Naira a Babban Birnin Jihar Kwara
- Wata gobara da ta faru a kasuwar Ita Amodu da ke Ilorin, babban birnin jihar Kwara ta lakume kayan miliyoyin Naira
- Hukumar kwana-kwana ta bayyana cewa jami'anta sun kai ɗauki a kan lokaci kuma sun yi nasarar daƙile yaɗuwar gobarar
- Mai magana da yawun hukumar, ya ce sun gano cewa wutar ta kama ne sanadiyyar haɗuwar mota da babbar wayar lantarki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kwara - Wata gobara da ta tashi a kasuwar Ita Amodu da ke kan tsohon titin Yidi a birnin Ilorin na jihar Kwara, ta lalata kayayyakin miliyoyin Naira.
Gobarar da ta afku a ranar Talata, ta takaita mazauna yankin da ’yan kasuwa da ke sayar da katifu, dadduma da sauran kayayyaki.
Jami'in hulɗa da jama'a ɓa hukumar kwana-kwana, Hassan Adekunle, ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda gobara ta jawo asara a jihar Kwara
Adekunle ya ce jami'an kwana-kwana sun yi ƙoƙarin kashe gobarar wacce ta samo asali daga wata babbar mota makare da katifu.
"Wutar ta babbake motar sannan ta yaɗu zuwa wani gini mai shaguna 19 da ɗakuna 47. Duk da tsananin gobarar jami'an mu sun kai ɗauki a lokacin da ya dace "
"Mun yi nasarar tseratar da shaguna 12 da ɗakuna 31 yayin da shaguna bakwai da ɗakuna 16 kuma ibtila'in gobarar ya taɓa su."
Abin da ya jawo gobara a Ilorin
Adekunle ya ce bincike ya nuna gobarar ta kama ne lokacin da motar katifu ta yi karo da babbar wayar wutar lantarki, tartsatsi ya tashi kuma nan take katifun suka kama da wuta.
Bugu da ƙari, kakakin hukumar ya kara da cewa fashewar taransufomar da ke kusa da kasuwar ya kara dagula lamarin, har wutar ta yaɗu zuwa shaguna, Channels tv ta kawo.
Gobara ta yi ɓarna a jihar Yobe
A wani labarin, kun ji cewa ‘yan kasuwar Bayan Tasha da ke Damaturu a jihar Yobe, sun wayi gari da iftila’in mummunan gobarar cikin dare.
Shaidar gani da ido ya bayyana cewa wutar na tashi da misalin 3: 00 na safe jim kadan bayan an dawo da wutar lantarki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng