Tinubu Ya Saurari Kukan Jama'a kan Ƙudirin Haraji, Ya ba da Sabon Umarni
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada aniyar tabbatar da adalci a kan kudirin haraji da ke gaban majalisar tarayya
- Ministan labarai, Mohammed Idris ya bayyana cewa gwamnati ta buɗe kofa domin karɓar shawarwari kan kudirin
- Shugaba Tinubu ya umarci ma’aikatar shari’a ta yi aiki tare da majalisa domin magance duk wata matsala ko korafi da aka shigar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce kudirin haraji da ake tattaunawa a majalisa yana da manufar kawar da matsalolin kuɗi a Najeriya tare da tallafawa jihohi da kananan hukumomi.
Ministan yada labarai da wayar da kan al’umma, Mohammed Idris ya ce ana buƙatar goyon bayan duk masu ruwa da tsaki domin cimma nasarar kudirin.
Ma'aikatar yada labarai ta wallafa a Facebook cewa shugaba Tinubu ya yi umurni a yi aiki tare da majalisa wajen duba korafe-korafen jama’a domin tabbatar da an yi gyaran da ya dace kafin zartar da kudirin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudirin haraji: Tinubu ya yabi 'yan Najeriya
Shugaba Tinubu ya yabawa yadda ‘yan Najeriya daga sassa daban-daban ke fitowa suna bayyana ra’ayoyinsu kan kudirin haraji, yana mai cewa hakan alama ce ta dimokuraɗiyya na aiki.
Ya yi kira ga duk masu ruwa da tsaki su guji hayaniya ko amfani da kalaman batanci yayin bayyana ra’ayoyinsu kan batutuwan da ke tasowa daga kudirin.
'Babu cutarwa a kudirin haraji' inji gwamnati
Channesls Television ya wallafa cewa ministan labarai ya karyata jita-jitar cewa gwamnati na ƙoƙarin gaggauta aiwatar da kudirin ba tare da la’akari da ra’ayoyin jama’a ba.
Ministan ya kara da cewa kudirin harajin ba zai tauye hakkin kowace jiha ba, a maimakon haka zai taimaka wajen rarraba albarkatu ga jihohi da kananan hukumomi.
Umarnin Tinubu kan gyaran kudirin haraji
Tinubu ya umarci ma’aikatar shari’a da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki su yi aiki tare da majalisar wajen magance matsalolin da aka gano a cikin kudirin haraji.
Shugaban ya ce wannan matakin yana nuna cewa gwamnati ta buɗe kofa ga shawarwari masu amfani domin tabbatar da cewa an cimma matsaya mai amfani ga dukkan ‘yan Najeriya.
Pantami: 'A dakatar da kudirin haraji'
A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Isa Ali Pantami ya yi kira ga majalisar tarayya da ta dakatar da kudirin dokar gyaran haraji domin sake nazari mai zurfi.
Tsohon ministan tarayyar ya ce akwai wasu sassa a cikin kudirin da suke bukatar sake nazari da shawara daga masu ruwa da tsaki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng