Ana Batun Kudirin Haraji, Sarkin Musulmi Ya ba 'Yan Najeriya Shawara

Ana Batun Kudirin Haraji, Sarkin Musulmi Ya ba 'Yan Najeriya Shawara

  • Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ba ƴan Najeriya shawara kan zamantakewa
  • Sarkin Musulmin ya buƙaci ƴan Najeriya da su riƙa amfani da dukiyoyinsu wajen taimakom mabuƙata da marasa galihu
  • Alhaji Sa'ad III ya yi kira da a ci gaba da gudunmawa wajen samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga ƴan Najeriya da su rungumi halin kyautatawa junansu.

Sarkin Musulmin ya buƙaci ƴan Najeriya da su riƙa raba dukiyoyinsu ga marasa galihu a cikin al’umma.

Sarkin Musulmi ya ba da shawara
Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya bukaci a rika taimakon mabukata Hoto: Sultanate Council Media Team
Asali: Facebook

Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ba da wannan shawarar ne a Abuja, ranar Talata yayin taron majalisar ƙungiyar addinai ta Najeriya (NIREC), cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara Sarkin Musulmi ya ba ƴan Najeriya?

Kara karanta wannan

Sheikh Ahmad Gumi ya fadi matsayarsa kan kudirin harajin gwamnatin Tinubu

Ya bukaci masu ruwa da tsaki da su ci gaba da ba da gudummawa wajen samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya, rahoton New Telegraph ya tabbatar da hakan.

Sarkin Musulmin ya tunatar da ƴan Najeriya cewa dukiyoyi abu ne na wucin gadi, kuma ya kamata a riƙa cin gajiyarsu tare da waɗanda Allah bai wadata musu ba.

"Na yi imanin cewa har yanzu muna da gudummawa mai yawa da za mu ba da ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasarmu."
"Mun san halin ƙuncin da kowa ke ciki. Mun san babu sauƙi. Amma Allah zai kawo sauƙi, domin ko wace irin wahala na tare da sauƙi. Zaman lafiya zai samu kuma abubuwa za su gyaru.
"Mu ci gaba da addu’a, kuma mu yi imani cewa Allah Maɗaukakin Sarki, wanda ya kawo mu cikin duniya, ba zai taɓa bari mu sha wahala ba."
"Mu duba yadda za mu taimakawa mabuƙata. Wannan watan Disamba ne, watan ƙarshe na shekara."

Kara karanta wannan

Jerin gwamnoni da manyan ƴan siyasar Arewa da suka ɗauki zafi kan ƙudirin harajin Tinubu

"Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya yi mana jagora ya kuma kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasarmu mai girma ta Najeriya.

- Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III

Sarkin Musulmi ya ba ƴan siyasar Sokoto shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya bayyana abin da ya kamata Sokoto ta koya daga makwabciyarta jihar Kebbi.

Sarkin Musulmin wanda tsohon soja ne ya buƙaci Sokoto da ta koyo irin salon siyasar haɗin kai da jihar Kebbi take da shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng