Hayaniya Ta Ɓarke a Majalisar Wakilai kan Kudirin Sauya Fasalin Harajin Tinubu
- Wata ƴar hayaniya ta ɓarke a zauren Majalisar wakilai kan kudirin sauya fasalin haraji da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya gabatar
- Lamarin ya fara ne lokacin da mai magana da yawun majalisar, Hon Akin Rotimi ya ambaci kudirin yayin gabatar da kansa a zaman yau
- Sai dai daga karshe, Rotimi ya janye kalamansa bayan ƴan majalisar wakilan tarayyar sun nuna rashin jin dadinsu a fili
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Rahotanni sun nuna cewa hayaniya ta ɓarke a zauren Majalisar wakilai a lokacin da Hon. Akin Rotimi ya kawo batun kudirin sauya fasalin haraji.
Rotimi, mai magana da yawun majalisar wakilai, ya mike ne da nufin gabatar da rahoto a madadin abokin aikinsa, Boma Goodhead, wanda bai halarci zaman yau Talata ba.
Me ya haddasa hayaniya a Majalisa?
Ɗan majalisar ya haddasa hayaniya da ce-ce-ku-ce a tsakanin mambobi lokacin da ya furta cewa ƴan jihar Ekiti sun goyi bayan kudirin haraji, The Cable ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akin Rotimi ya ce:
"Sunana Akin Rotimi Jr, ina wakiltar Ekiti ta arewa. Ya mai girma shugaban majalisa, ni dan jihar Ekiti ne, jiha ta farko da ’yan majalisar wakilanta gaba daya suka amince da kudirin haraji."
Yana furta haka sauran ƴan majalisa suka katse shi, suka fara hayaniya da ce-ce-ku-ce mai zafi a zaman yau Talata, 3 ga watan Disamba.
Shugaban Majalisa ya kwantar da hankula
Shugaban majalisar, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, wanda ya jagoranci zaman, ya yi ƙoƙarin kwantar da hankula, inda ya ce Rotimi ya faɗi ra'ayinsa kansa ne.
‘Yan majalisar dai ba su ji dadin kalaman da Rotimi ya furta ba, inda suka yi ta ihun cewa, “a’a, a’a, a’a."
Sai dai daga baya, Akin Rotimi ya bai wa sauran abokan aikinsa hakuri tare da janye kalaman da ya yi kan kudirin harajin.
"Mai girma kakakin majalisa na janye gabatarwar da na yi, zan yi yadda ya dace, dan Allah a bari na yi magana, abokan aiki, na janye kalaman da na faɗa," in ji shi.
'Majalisa za ta amince da kudirin haraji'
Rahoto ya gabata cewa Sanata Seriake Dickson mai wakiltar Bayelsa ta Yamma ya ce majalisa za ta amince da sabon kudirin haraji na Bola Tinubu.
Tsohon gwamnan jihar Bayelsa ya ce ko sama da ƙasa za su haɗu sai sun zartar da dokar sauya fasalin haraji kamar yadda aka yi a dokar PIA.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng