An Samu Budurwa Mai Shekaru 19 Tsirara bayan Kubuta daga Hannun Masu Tsafi
- Hukumar NSCDC a Kwara ta ceto ɗaliba mai shekaru 19 da ke karatu a jami'ar jihar Kogi bayan zargin matsafa sun sace ta
- Rahotanni na nuni da cewa an gano Fauziyah Mohammed ne tana yawo a tsirara a unguwar Ajegunle-Isale a birnin Ilorin
- An tabbatar da cewa gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya yi alƙawarin taimaka mata wajen komawa jiharta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kwara - A yau Talata hukumar NSCDC a Kwara ta ceto ɗaliba 'yar aji hudu a jam'iar jihar Kogi bayan an sace ta.
Wata majiya ta bayyana cewa ana zargin an sace dalibar ne mai suna Fauziyah Mohammed 'yar shekaru 19 domin yin tsafi.
Rahoton jaridar the Guardian ya nuna cewa wasu mutane ne suka ga dalibar suka mika ta ga jami'an NSCDC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fauziyah ta ce ba ta san yadda ta tsinci kanta a Kwara ba, amma ta tuna cewa ta rasa sanin inda take yayin da ta yi yunƙurin ɗaukar littafi da ya faɗi daga hannunta.
An samu budurwa tsirara a Kwara
Kwamandan NSCDC, Dr Umar Mohammed ya ce mazauna yankin Ajegunle-Isale ne suka gano Fauziyah tana yawo tsirara kuma suka sanar da jami’ai.
Dr Mohammed ya ce bayan an kawo ta gare su, sun ba ta tufafi tare da bata kwarin gwiwa kan matsalar da ta tsinci kanta a ciki.
A karon farko, Fauziyah ba ta cika magana mai ma’ana ba, lamarin da ya sa jami’an NSCDC suka yanke hukuncin cewa ta gamu da mummunan abu yayin da take hannun masu tsafin.
An samu dalibar jami'ar Kogi a Kwara
Kwamandan ya ƙara da cewa gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya yi alkawarin taimakawa wajen dawo da Fauziyah zuwa jiharta ta Kogi.
The Nation ta ruwaito cewa NSCDC ta ce za ta damƙa Fauziyah ga wani mai suna Salihu Aliu, wanda iyalanta suka turo domin karɓar ta.
NSCDC ta kama mai taimakon 'yan bindiga
A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni da suka fito daga jihar Kwara na nuni da cewa masu garkuwa da mutane sun sace wata uwa da ‘ya’yanta biyu a garin Ajase-Ipo.
A wata nasara da suka samu, jami'an hukumar NSCDC sun kama wanda ake zargi da ba wa masu garkuwar bayanai, Abu Usman Soja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng