NPower: Majalisar Tarayya Ta ba Tinubu Sa'o'i 72 Ya Buɗe Asusun Hukumar NSIPA
- Majalisar wakilai ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin buɗe asusun hukumar NSIPA daga nan zuwa sa'o'i 72 masu zuwa
- Ta ɗauki wannan matakin ne bayan amincewa da kudirin da mataimakin kakakin majalisa, Benjamin Kalu da yan majalisa 20 suka gabatar
- Hon. Kalu ya shaidawa majalisa yayin gabatar da kudirin cewa hukumar na taimakawa wajen yaƙar fatara da tallafawa matasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Majalisar wakilai ta tarayya ta buƙaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bude asusun hukumar kula da walwalar al'umma watau NSIPA.
Majalisar ta roƙi shugaban kasa ya umarci ministan kudi da harkokin tattalin arziki, Wale Edun, ya buɗe asusun hukumar daga nan zuwa sa'o'i 72.
Ƴan majalisar wakilan sun cimma wannan matsaya a zamansu na yau Talata, 3 ga watan Disamba, 2024, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisa ta umarci buɗe asusun NSIPA
Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da Benjamin Kalu, mataimakin kakakin majalisar da wasu ‘yan majalisa 20 suka dauki nauyi.
Shirye-shiryen walwala da jin daɗin al'umma da ke ƙarƙashin hukumar NSIPA sun haɗa da N-Power, shirin tallafin kudi na CCT, tallafin masana'antu da ciyar da ɗalibai.
Majalisar ta bayyana cewa buɗe asusun hukumar zai ba da damar sake farfaɗo da shirye-shiryen tallafi waɗanda ke taka rawa wajen ragewa ƴan ƙasa radaɗi.
Majalisa ta buƙaci Tinubu ya saki kudin N-Power
Har ila yau, majalisar ta bukaci Shugaba Tinubu ya tabbatar da an saki kuɗi domin biyan masu cin gajiyar N-Power su 395,731 haƙƙoƙinsu da aka riƙe, Rahoton Daily Trust.
Da yake gabatar da kudirin, Kalu ya ce hukumar na da muhimmanci a ƙoƙarin kawar da talauci, tallafawa matasa da wasu shirye-shiryen ragewa ƴan kasa raɗadi.
"Sakamakon rufe asusun NSIPA, shirin N-Power ya tsaya cak tare da riƙe alawus na masu cin gajiyar shirin su 395,731 kimanin N81,315, 440,000."
"Waɗannan kuɗaɗe na ƴan N-Power na cikin kasasfin kudin 2023 da 2024, wanda za a gama aiwatar da su ranar 31 ga watan Satumba, 2024," in ji Kalu.
Majalisa ta sa baki kan shirin bankin CBN
A wani rahoton, an ji cewa Majalisar wakilai ta bukaci babban bankin Najeriya (CBN) da ya dakatar da shirinsa na yi wa ma’aikata har 1,000 ritaya
Dan majalisar daga jihar Ebonyi, Hon Kama Nkemkama ya gabatar da kudurin inda ya nuna damuwa kan rashin tsari a ritayar.
Asali: Legit.ng