'Kudirin Haraji Zai Iya Jefa Najeriya a Tashin Hankali,' Dattijo Ya yi Gargadi

'Kudirin Haraji Zai Iya Jefa Najeriya a Tashin Hankali,' Dattijo Ya yi Gargadi

  • Kudirin gyaran haraji na Bola Tinubu na cigaba da jan hankalin masu ruwa da tsaki daga yankuna daban-daban na kasar nan
  • Wani shugaban kungiya mai rajin kishin kasa, Dr. Sani Shinkafi ya caccaki gwamnonin da ke adawa da kudirin gyaran harajin
  • Jagora a Kudancin Najeriya, Edwin Clark ya yi gargadin cewa rashin kula da nazari kan kudirin zai iya haifar da matsaloli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kungiyar Patriots for Advancement of Peace and Social Development, Dr Sani Shinkafi, ya caccaki gwamnonin jihohi da ke adawa da kudirin haraji.

Dr Sani Shinkafi ya bayyana gwamnonin a matsayin masu gazawa wajen samar da hanyoyin samun kudaden shiga a jihohinsu.

Edwin Clark
Edwin Clark ya bukaci a yi taka tsan tsan da kudirin haraji. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Sani Shinkafi ya ce adawar gwamnonin ta samo asali ne daga tsoron rasa samun kudi sosai daga gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Kudirin haraji: An fara samun rabuwar kai tsakanin gwamnonin Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata hira da ya yi da Arise News, Dr Shinkafi ya soki kungiyar Northern Youth Assembly da ta yi tir da kudurin.

Shinkafi ya yi kaca kaca da gwamnoni

Dr. Shinkafi ya ce saboda za a dawo raba kudaden haraji da aka tattara bisa gudunmawar jihohi, shi ya sa gwamnonin Arewa suke kuka.

A cewarsa, yawancin gwamnonin ba su shirya bunkasa jihohinsu domin samun kudaden shiga ba, kuma shi ya sa suke korafi.

Ya kuma kare kudirin gyaran harajin yana mai cewa ita ce hanya mafi dacewa domin habaka tattalin arzikin kasar nan.

Edwin Clark ya yi gargadi kan tsoron rikici

A daya bangaren, babban jigo a Kudancin Najeriya, Cif Edwin Clark ya yi gargadi cewa rashin nazari wajen aiwatar da kudirin na iya jefa kasar cikin matsaloli.

Clark ya ce batun kudirin gyaran haraji abu ne da ke bukatar kulawa ta musamman domin rashin kula da shi zai iya kawo rikice-rikice.

Kara karanta wannan

"Abin da ya kamata Tinubu ya yi kan gyaran haraji," Dan majalisar Arewa ya magantu

Tsohon ministan ya koka kan yadda yankin Arewa da Kudu maso Yamma suka mamaye maganar haraji, ya ce kamar an ware sauran yankunan kasar.

Jihohi sun yi sabani kan kudirin haraji

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin jihohi na cigaba da bayyana ra'ayoyi kan kudirin harajin da Bola Tinubu ya aika gaban majalisun Najeriya.

Jihohi kamar Kogi da Benue sun goyi bayan kudirin dokar gyaran harajin yayin da Borno, Nasarawa da Kano suka soke ta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng