Yajin Aiki: NLC Ta Yi Martani ga Gwamnan da ke Shirin Korar Ma'aikata cikin Kwanaki 3

Yajin Aiki: NLC Ta Yi Martani ga Gwamnan da ke Shirin Korar Ma'aikata cikin Kwanaki 3

  • Kungiyar kwadago ta NLC ta yi martani ga kalaman gwamna Francis Nwifuru na korar ma'aikatan da ke yajin aiki
  • Haka kuma gwamnatin Ebonyi ta ce za ta iya kin biyan ma'aikatan albashi na adadin kwanakin yajin aikin da su ka yi
  • Shugaban NLC na kasa, Kwamred Joe Ajaero ya ce ba kai tsaye su ka tsunduma yajin aiki ba, sai da aka gaza cimma matsaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ebonyi - Shugaban Kungiyar Kwadago ta kasa (NLC), Joe Ajaero, ya yi Allah-wadai da barazanar da gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ke yi ga ma’aikata.

Gwamnan ya fara barazana ga ma’aikatan ne bayan sun tafi yajin aikin gargadi saboda kin biyansu mafi karancin albashi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Neja ya fara biyan albashin da ya fi na sauran jihohin Arewa ta Tsakiya

Kwadago
NLC ta soi gwamnati kan ikirarin korar ma'aikata Hoto: NLC HQ/Francis Ogbonna Nwifuru
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa gwamna Francis Nwifuru ya yi barazanar korar ma’aikatan da suka shiga yajin aiki ko kin biyan su albashi na lokacin yajin aikin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar NLC ta soki gwamnan Ebonyi

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa kungiyar kwadago ta kasa ta yi tir da matakin da gwamnan Ebonyi ke shirin dauka a kan ma'aikatan da ke neman hakkinsu.

Shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero ya zargi gwamnatin jihar, karkashin Francis Nwifuru da kin tattaunawa da shugabannin kwadago domin cimma matsaya.

Ebonyi: Dalilin NLC na tafiya yajin aiki

Kungiyar NLC ta bayyana cewa gwamnati ta gaza amincewa a samu matsaya a kan batun albashin ma'aikatan jihar.

Kwamred Joe Ajaero ya ce;

“Yajin aikin ya biyo bayan rashin nasara a zaman da aka yi a baya."

Ya kara da cewa doka ta ba ma'aikata dama su nuna rashin jin dadinsu ta hanyar gudanar da yajin aiki makama

Kara karanta wannan

Ma'aikata za su cigaba da jira, Gwamnan Zamfara zai fara biyan mafi ƙarancin albashi a 2025

Kungiyar NLC ta shiga yajin aiki

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar kwadago ta NLC ta fara gudanar da yajin aiki a wasu jihohi, bayan sun gaza aiwatar da mafi karancin albashin N70,000 ga ma'aikata.

Ma'aikatan sun fara yajin aikin gargadi a jihohin da su ka hada da Kaduna, Nasarawa, Ebonyi, da Cross Rivers, a yunkurin da tilastawa gwamnatocin jihohin biyansu mafi karancin albashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.