Kudirin Haraji: An Fara Samun Rabuwar Kai Tsakanin Gwamnonin Arewa
- Gwamnonin jihohi na cigaba da bayyana ra'ayoyi kan kudirin harajin da Bola Tinubu ya aika gaban majalisun Najeriya
- Jihohi kamar Kogi da Benue sun goyi bayan kudirin dokar gyaran harajin yayin da Borno, Nasarawa da Kano suka soke ta
- Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya yi gargadin cewa aiwatar da kudirin na iya yin illa ga miliyoyin 'yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Arewa - Wasu jihohin Arewacin Najeriya sun rabu kan kudirin gyaran haraji da ke gaban majalisar tarayya.
Jihohin da suka bayyana goyon bayansu sun haɗa da Kogi da Benue yayin da Borno, Nasarawa, da Kano suka nuna rashin goyon baya.
Vanguard ta hada rahoton kan cewa wasu jihohi a Najeriya sun ce har yanzu suna nazarin dokar domin yanke matsaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudirin haraji: Jihohin Arewa sun fadi ra’ayoyinsu
Rahoton Channels Television ya nuna cewa gwamna Babagana Zulum ya nuna damuwa kan kudirin haraji, yana mai cewa zai iya yin illa ga miliyoyin ‘yan Najeriya.
A Nasarawa, Gwamna Abdullahi Sule ya yi tsokaci kan tsarin rabon harajin VAT da aka tsara a kudirin, ya ce shi ne babbar matsalarsu.
Jihohin Kano da Benue kan kudirin haraji
Majalisar dokokin jihar Kano ta yi watsi da kudirin gyaran haraji bayan tattaunawa a zaman ta na jiya karkashin jagorancin kakakin majalisar, Ismail Jibrin Falgore.
Kwamishinan kudi da tsare-tsaren tattalin arziki a Benue, Michael Oglegba, ya bayyana goyon bayan gwamnatin jihar ga kokarin gwamnatin tarayya na inganta haraji.
“Kudirin gyaran haraji babban abu ne da ya dace. Muna goyon bayan kokarin gwamnati na bunkasa kudin shiga.”
- Michael Oglegba
Ma’aikatar Kudi da tsare tsaren tattalin arziki a jihar Kogi ta shirya taron tattaunawa da al’umma kan kudirin, inda ta bayyana cikakken goyon baya ga Bola Tinubu.
Pantami ya bukaci dakatar da kudirin haraji
A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Isa Ali Pantami ya yi kira ga majalisar tarayya da ta dakatar da kudirin dokar gyaran haraji domin sake nazari mai zurfi.
Tsohon ministan tarayyar ya ce akwai wasu sassa a cikin kudirin da suke bukatar sake nazari da shawara daga masu ruwa da tsaki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng