Zulum Ya Gargadi Tinubu, Ya Fadi Abin da Zai Faru Idan Ya Zartar da Kudirin Haraji
- Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya sake nuna illar da ke tattare da ƙudirin harajin gwamnatin Bola Tinubu
- Farfesa Zulum ya nuna cewa ƙudirin zai yi wa ƴan Najeriya illa idan shugaba Tinubu ya yi amfani da ikonsa wajen zartar da shi
- Gwamnan ya bayyana cewa idan dai ƙudirin ya zama doka a Najeriya, wasu jihohi kawai zai amfana yayin da za a bar sauran a baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya gargaɗi Shugaba Bola Tinubu kan ƙudirin haraji.
Gwamna Zulum ya ce duk da cewa Tinubu na da ikon aiwatar da ƙudirin haraji, amma yin hakan na iya haifar gagarumar illa ga miliyoyin ƴan Najeriya.
Ana ta adawa da ƙudirin harajin Tinubu
Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar Channels tv a shirinsu na 'Sunday Politics' a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙudirin harajin wanda da ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa yana fuskantar turjiya musamman daga manyan Arewa.
Ƙungiyoyi irinsu ƙungiyar gwamnonin Arewa, ƙungiyar dattawan Arewa, majalisar tatttalin arziƙi ta ƙasa (NEC) da Sanata Mohammed Ali Ndume sun bukaci a janye shi.
Wane gargaɗi Zulum ya yi wa Tinubu?
A yayin hira da gwamnan na Borno, ya bayyana cewa shugaba Tinubu, na da ikon zartar da ƙudirin, amma fa akwai abin da zai biyo ba ga ƴan Najeriya.
"Mun san ikon shugaban ƙasa. Ni mutum ne mai bin tsari, Ina girmama shi."
"Idan har shugaban ƙasa yana son yin amfani da ƙarfin ikonsa wajen zartar da ƙudirin haraji, to zai iya yin hakan, amma yana da illa ga jama’a."
"Muna cikin dimokuraɗiyya. Ya kamata mu fahimci abin da wannan tsarin harajin ya ƙunsa. Wannan shi ne kawai abin da muke cewa."
- Gwamna Babagana Umara Zulum
Zulum ya kuma bayyana cewa jihohi biyu na Legas da Rivers ne kawai za su ci gajiyar wannan sabon tsarin harajin.
Ƙungiya za ta yi wa Zulum da Ndume addu'o'i
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar Southern Borno Concerned Citizens (SBCCs), ta shirya gudanar da azumi domin karramawa da nuna goyon baya ga Gwamna Babagana Zulum da Sanata Ali Ndume.
Ƙungiyar ta yi kira ga mambobinta a fadin ƙananan hukumomi tara da waɗanda ke zaune a ƙasashen waje da su gudanar da azumin na rana ɗaya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng