'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 9, Sun Yi Awon Gaba da Wasu Masu Yawa a Wani Hari
- Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a ƙauyen Dan Tudu na ƙaramar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto
- Maharan sun hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba, suka tura mutane masu yawa zuwa cikin daji
- Majiyoyi sun bayyana ƴan bindigan da suka kawo harin na ƙarƙashin jagorancin Bello Turji da wasu hatsabiban ƴan ta'adda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai mummunan hari a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.
Ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Dan Tudu inda suka kashe mutane tara tare da raunata wani mutum ɗaya.
Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan bindiga suka kai hari a Sokoto
Ya bayyana cewa ƴan bindigan sun kuma yi garkuwa da mutane masu yawa da suka haɗa da mata da maza.
Ƴan bindigan sun kuma sace wasu kayayyaki masu yawa waɗanda da ba za a iya bayyana adadin ƙudinsu ba.
Majiyoyi sun bayyana waɗanda suka aikata wannan aika-aika a matsayin ƴan bindigan da ke ƙarƙashin jagorancin Saidu Zango, Bello Turji, da Jammo Baki, waɗanda aka sansu da gudanar da ayyukansu a yankin Gangara.
An bayyana cewa ƴan bindigan sun riƙa shiga gidaje, suke sace dabbobi, kuɗi, da sauran kayayyaki kafin su tafi da mutanen da suka yi garkuwa da su zuwa cikin daji.
Ƴan bindiga dai na yawan kai hare a ƙauyukan wasu ƙananan hukumomin jihar Zamfara.
Dakarun ojoji sun hallaka ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta samu nasarar kai hare-hare kan ƴan bindiga a jihar Zamfara.
Hare-haren da sojojin suka kai ta sama a ƙauyen Babban Kauye da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, ya yi nasarar kashe ƴan bindiga da dama tare da lalata maɓoyarsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng