Gobara Ta Tashi a Babbar Kasuwa a Abuja, Ta Yi Barna Mai Yawa

Gobara Ta Tashi a Babbar Kasuwa a Abuja, Ta Yi Barna Mai Yawa

  • An samu tashin wata mummunar gobara a kasuwar da ke rukunin gidajen Trademore, a Lugbe cikin birnin tarayya Abuja
  • Gobarar wacce ta tashi a cikin tsakar dare, ana zargin ta auku ne sakamakon matsalar wutar lantarki
  • Jami'an ba da agajin gaggawa sun samu nasarar shawo kanta tare da hana yaɗuwarta, sa'o'i biyu bayan ta tashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wata mummunar gobara ta tashi a kasuwar da ke rukunin gidajen Trademore, a Lugbe, cikin birnin Abuja.

Gobarar dai ta tashi ne a kasuwar guda ɗaya tilo da ke a rukunin gidajen a daren ranar Lahadi.

Gobara ta tashi a wata kasuwa a Abuja
An samu tashin gobara a Abuja Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Tashar talabijin ta Channels tv ta ruwaito cewa gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 3:30 na dare jim kaɗan bayan dawo da wutar lantarki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gobara ta yi ɓarna a birnin Abuja

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a shahararriyar kasuwa a Legas, ta yi barna

Gobarar ta mamaye kasuwar kafin jami’an agaji su kai ɗauki zuwa wajen.

Yayin da har yanzu ba a san ainihin musabbabin tashin gobarar ba, shaidun gani da ido na zargin lamarin ya auku ne saboda matsalar wutar lantarki.

Jaridar The Punch ta ce wata mazauniyar wajen mai suna Vanguard Joe, wacce tana daga cikin waɗanda suka fara ganin gobarar, ta bayyana lamarin a matsayin tashin hankali.

"An sanar da ni da misalin ƙarfe 4:00 na dare, kuma zuwa lokacin, wutar ta riga ta bazu. Ba mu iya tantance abin da ya haddasa ta ba, amma muna zargin matsalar wutar lantarki ce."

- Vanguard Joe

Jami'ai sun kai agajin gaggawa

Ta ƙara da cewa jami'an kashe gobara na cocin Dunamis, na EFCC da waɗanda ke aiki a tashar Sauka ne suka kawo agajin gaggawa.

"Sa’o’i biyu bayan tashin gobarar, a ƙarshe jami’an bayar da agajin gaggawa sun shawo kan lamarin, inda suka kashe wutar tare da hana yaɗuwar ta."

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a ofishin gidan rediyon Najeriya, an gano abin da ya faru

- Vanguard Joe

Gobara ta tashi a gidan rediyon Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin gobara a harabar ofishin gidan Rediyon Najeriya da ke Legas a yankin Kudu maso Yamma.

Gobarar dai ta tashi ne a ranar Laraba, 27 ga watan Nuwamban 2024 a harabar ofishin da ke Lamba 35, kan titin Ikoyi a Legas, lamarin da ya haifar da fargaba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng