Kalubalen APC na Kara Kamari, Wasu Sun Balle don Kafa Sabuwar Jam'iyya

Kalubalen APC na Kara Kamari, Wasu Sun Balle don Kafa Sabuwar Jam'iyya

  • Jam'iyyar APC ta kara fadawa matsala bayan wasu daga cikin magoya bayanta sun fara nuna adawa da salon mulkin Bola Tinubu
  • Kungiyar TNN da ke goyon bayan APC ta ce ta dawo daga rakiyar gwamnatin tarayya, ganin halin da kasa ta shiga na talauci
  • Shugaban kungiyar, Modibbo Farakwai ya shaidawa manema labarai a Kano cewa su na shirin korar APC daga mulki a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - APC ta samu babbar baraka, yayin da aka samu tsakin da ya balle domin samar da sabuwar jam’iyyar siyasa a kasar nan.

Team New Nigeria (TNN) ta bayyana rashin gamsuwa da yadda APC ke mulkin kasar, tare da shirin yin rajista da hukumar zabe ta kasa (INEC).

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta sauya magana, ta fadi mamallakin shinkafar 'Tinubu' da aka kama

Ganduje
Wasu 'yan siyasa na shirin yi wa APC kishiya Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR/Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa shugaban TNN na kasa, Modibbo Farakwai, shi ne ya bayyana shirin kungiyar na zama jam’iyyar siyasa a Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin TNN na ballewa daga jam'iyyar APC

Jaridar This day ta wallafa cewa kungiyar TNN ta yi takaicin yadda APC ta ke watsi da wadanda aka kafa jam'iyya da su, tare da ba ta gudunmawa.

Shugaban kungiyar, Modibbo Farakwai da ya bayyana haka, ya kara da cewa karuwar talauci da jama'a ke ciki, babbar nakasu ce ga gwamnatin Tinubu.

Zaben 2027: TNN na son kayar da APC

Kungiyar TNN ta ce ta fahimci matsalolin da su ka hana kasar nan cigaba, gami da hanyoyin magance su domin samar da cigaba mai dorewa.

A cewar Farakwai, TNN ta fara shirin tattara miliyoyin 'yan Najeriya daga shiyyoyi shida na kasar don kwace mulki daga APC a zaɓen 2027.

APC ta ki karbar sababbin 'yan siyasa

Kara karanta wannan

Jagora a PDP ya fusata, ya 'fallasa' masu kunno mata rigimar cikin gida a Kano

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyya mai mulki ta APC ta watsawa wadansu 'yan adawa a ido, bayan sun bar tsohuwar jam'iyyarsu, tare da yunkurin komawa cikinta a jihar Ondo.

Lamarin ya faru makonni bayan gwamna Lucky Aiyedatiwa ya yi nasarar lashe zaben gwamnan jihar, inda kusoshin APC a gundumar Ogbagi da ke Akoko su ka karbar masu son shiga cikinta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.