Zulum Ya Fadi Dalilin Gwamnonin Arewa Na Son a Dakatar da Kudirin Haraji
- Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana dalilin gwamnonin Arewa na son dakatar da ƙudirin haraji
- Zulum ya bayyana cewa gwamnonin na buƙatar lokaci domin yin shawarwar kan ƙudirin wanda ke gaban majalisar dattawa
- Ya ce idan har aka amince da ƙudirin, to jihar Legas ce kaɗai za ta amfana da tsarin yayin da sauran jihohi kuma za su zama ƴan kallo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya sake yin magana kan ƙudirin haraji na Shugaba Bola Tinubu.
Gwamna Zulum ya bayyana dalilin da ya sa gwamnonin Arewa suka shawarci shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da ya saurara kafin ya tura daftarin ƙudirin sake fasalin haraji.
Gwamna Zulum ya yi magana ne a yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Sunday Politics', a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me gwamna Zulum ya ce kan ƙudirin haraji
Zulum ya bayyana cewa ƙungiyar gwamnonin Arewa na buƙatar lokaci ne kawai domin yin shawarwari.
"A kan wannan batun haraji, akwai kura-kurai da yawa. Mun ji cewa tanadin VAT a cikin dokar haraji, bisa ƙididdigar da muka yi, jihohin Legas da Rivers ne kaɗai za su ci gajiyar wannan tsarin."
"Mun yi namu binciken kuma muka yanke cewa asara za mu yi. Me yasa muke cikin gaggawa? Mun shawarci gwamnatin tarayya da ta dakata, ta cire wasu sharuɗɗan da za su cutar da Arewacin Najeriya."
"Abin da muke cewa shi ne a ba da isashshen lokaci, mu nemi shawarwari domin fahimtar duk abin da ke cikin wannan tsarin haraji kafin zartar da shi ya zama doka."
- Gwamna Babagana Umara Zulum
Zulum ya yi bayanin cewa idan har majalisar tarayya ta ƙasa ta amince da dokar, za a bar jihohi a baya domin jihar Legas ce ƙadai za ta ci gajiyar wannan tsarin.
Gwamna Zulum ya yi ƙarin albashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum ya amince da ƙarin albashi ga likitocin da ke aiki a ƙarƙashin gwamnatin jihar.
Gwamna Zulum ya amince a yi wa likitocin ƙari su koma suna karɓar albashi iri ɗaya da abinda ake biyan takwarorinsu a matakin tarayya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng