Abacha: Obasanjo Ya Yi Martani bayan Gowon Ya Fadi Yadda Ya Ceto Rayuwarsa

Abacha: Obasanjo Ya Yi Martani bayan Gowon Ya Fadi Yadda Ya Ceto Rayuwarsa

  • Tsohon shugaban ƙasan Najeriya ya yi martani ga Janar Yakubu Gowon bayan ya bayyana yadda ya roƙi Abacha ka da ya kashe shi
  • Obasanjo ya bayyana cewa duk da yana sane mutane da dama sun yi ƙoƙari domin a sake shi daga kurkuku, bai taɓa sanin irin wanda Gowon ya yi ba
  • Ya miƙa godiyarsa ga tsohon shugaban ƙasan bisa ƙoƙarin da ya yi domin ganin ya fito daga gidan kurkuku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya mayar da martani ga Janar Yakubu Gowon.

Obasanjo ya yi martanin ne bayan Gowon ya bayyana cewa ya roƙi marigayi Janar Sani Abacha, ka da ya kashe shi.

Obasanjo ya yi wa Gowon martani
Obasanjo ya yi martani ga Janar Yakubu Gowon Hoto: Caleb Mutfwang, Olusegun Obasanjo
Asali: Facebook

Obasanjo ya ce bai san cewa Gowon ya yi irin wannan ƙoƙarin ba, har sai da ya fito ya bayyana hakan, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun hallaka 'yan ta'adda 135, sun kubutar da mutane masu yawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane martani Obasanjo ya yi wa Gowon?

Tsohon shugaban ƙasan ya ce ya san mutane da dama sun yi ƙoƙari daban-daban domin ganin an sako shi, kuma bayan haka ya zagaya ya yi godiya a ciki da wajen ƙasar nan.

"Ina so na jinjinawa maigidana, Janar Yakubu Gowon. Jiya ya faɗi wani sirri kuma dole na gode maka musamman akan hakan."
"Lokacin da za fito daga gidan yari, na samu damar yin godiya ga abokai, a ciki da wajen ƙasar nan da suka ba da gudummawa wajen yin roƙo da addu'a domin a sake ni daga kurkuku."
"Kuma na zagaya duniya ina godiya ga waɗanda suka yi ta ba da baki da addu’a domin a sake ni daga kurkuku."
"Amma ban san cewa ka rubuta wasiƙa domin a sake ni ba sai da ka faɗa a jiya. Ina yi maka godiya saboda hakan."

- Olusegun Obasanjo

Obasanjo dai da tsohon shugaban ƙasa, marigayi Murtala Mohammed, sun hambarar da Yakubu Gowon a wani juyin mulki a ranar 29 ga watan Yuli, 1975.

Kara karanta wannan

Mutumin Gombe da ya niƙi gari ya tafi Abuja a keke ya samu kyautar mota da kudi

Obasanjo ya gargaɗi matasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya gargadi matasa da ɗalibai da su guji tu'ammali da miyagun ƙwayoyi, yana mai cewa ba su da amfani ga rayuwa.

Obasanjo ya yi wannan kiran ne a taron ‘Fly Above The High’ da ƙungiyar RAN ta shirya kan yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Abeokuta, jihar Ogun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng