"Mutane Sun Zama Mabarata," Jigon APC Ya Koka kan Tsadar Kayan Abinci a Najeriya

"Mutane Sun Zama Mabarata," Jigon APC Ya Koka kan Tsadar Kayan Abinci a Najeriya

  • Wani jigo a APC ya koka kan matsanancin kuncin rayuwar da ƴan Najeriya ke fuskanta sakamakon tashin farashin kayan abinci
  • Mr Olatunbosun Oyintiloye ya ce duk da koƙarin da gwamnatin Bola Tinubu ke yi, galibin magidanta ba su iya ciyar da iyalansu sau uku a rana
  • Ya roƙi gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohi su ƙara dagewa wajen sauƙaƙawa talakawa wannam halin da suka tsinci kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Wani jigon jam'iyyar APC a jihar Osun, Mr Olatunbosun Oyintiloye, ya ce tsadar kayan abinci ya fara zama bala'i a halin da ake ciki a ƙasar nan.

Oyintiloye, wanda yana ɗaya daga cikin ƴan kwamitin kamfen shugaban kasa na APC (PCC) da aka rushe, ya faɗi haka ne a wata hira da ƴan jarida a Osogbo.

Kara karanta wannan

CBN ya shirya share hawayen ƴan Najeriya, ya taso bankuna kan takardun Naira

Abinci.
Jigon APC ya koka kan tsadar kayan abinci, ya ce yan Najeriya na cikin ƙuncin rayuwa Hoto: Contributor
Asali: Getty Images

Jigon APC ya koka kan tsadar abinci

Ya koka kan cewa galibin magidanta ba su samun abinci mai kyau, wasu ma sai sun fita sun yi bara ko sun roƙa sannan za su ci, Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon APC ya ce akwai bukatar gwamnatoci a dukkan matakai su kawo daukin gaggawa ga talakawa ta hanyar samar da hanyoyin da za su kawar da fatara da yunwa.

Oyintiloye ya bayyana cewa farashin kayan abincin da ake ci na yau da kullun kamar shinkafa, wake, garri, semovita, fulawa, dawa da dai sauransu na nema ya fi ƙarfin talaka.

A cewarsa, ƴan Najeriya da dama ba su iya sayen waɗannan abincin saboda tsada, shiyasa suka koma cin duk abin da ya samu kawai don su rayu.

Ƴan Najeriya na cikin wahalar rayuwa

Jigon APC ya kuma ƙara da cewa duk da ƙoƙarin gwamnatin Bola Tinubu na sauke farashin abinci, mafi akasarin ƴan Najeriya ba su iya cin abinci sai uku a rana.

Kara karanta wannan

Badakalar N80.2bn: Kotu ta yi fatali da bukatar EFCC a shari'ar tsohon gwamnan Kogi

"Ina rokon gwamnoni da gwamnatin tarayya su kara ƙaimi wajen daƙile yawan tashin farashin kayan abinci," in ji shi.

Wani magidanci, Malam Sule Abdullahi, ya shaidawa Legit Hausa cewa a yanzu mutane sun daina tunanin komai sai abinci.

Mutumin mai sayar da kayan miya, ya ce:

"Wallahi ana cikin wahala fiye da tunani, taya za a samu abin da za a ci shi ne ajenda ta farko a wurin kowane maigida, maganar kuɗin makaranta, wuta da sauransu duk an jingine su.
"A yanzu akwai waɗanda suke fatan mutuwa da rayuwar da suke ciki, abin fa ya wuce tunaninka, ya kamata mutane su farka, wannan gwamnatin kashe mu take son yi da yunwa."

Duk da haka magidancin ya yi kira ga gwamnati ta sake tunani kan wasu matakan da ya ɗauka musamman tallafin mai.

Dattawan Arewa sun koka kan tsadar rayuwa

A wani labarin kun ji cewa Kungiyar dattawan Arewa ta ACF ta yi magana kan tsadar rayuwa da yan Najeriya ke cigaba da kuka a kai tun zuwan Bola Tinubu

Shugabannin kungiyar sun bukaci Bola Tinubu ya gaggauta sauya tsare tsaren da ya kawo domin ceto rayuwar miliyoyin yan Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262