NDLEA Ta Yi Babban Kamu, Dan Kasuwar da Ya Shigo da Hodar Iblis Ya Shiga Hannu

NDLEA Ta Yi Babban Kamu, Dan Kasuwar da Ya Shigo da Hodar Iblis Ya Shiga Hannu

  • Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) sun yi nasarar cafke wani ɗan kasuwa a jihar Legas
  • An cafke ɗan kasuwan ne wanda ya dawo daga ƙasar Brazil ɗauke da hodar iblis mai nauyin gram 700
  • Da ake masa tambayoyi ya bayyana cewa ya shigo da kayayyakin ne domin samun kuɗaden da zai bunƙasa kasuwancinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta ce ta kama wani ɗan kasuwa mazaunin ƙasar Brazil, Ezeokoli Sylva, ɗauke da hodar iblis.

Hukumar NDLEA ta cafke ɗan kasuwar ne ɗauke da gram 700 na hodar iblis a cikinsa, a filin jirgin sama na Murtala Muhammed, da ke Ikeja a jihar Legas.

Jami'an NDLEA sun yi kamu a Legas
Jami'an NDLEA sun cafke mai safarar hodar iblis Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

NDLEA ta cafke mai safarar hodar iblis

Daraktan yaɗa labarai na hedkwatar NDLEA da ke Abuja, Femi Babafemi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane masu yawa ciki har da jariri a Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Femi Babafemi ya bayyana cewa jami’an tsaro ne suka gano hakan a filin jirgin saman, a lokacin da wanda ake zargin ya dawo gida Najeriya bayan kwashe shekara 35 a Brazil, rahoton Punch ya tabbatar.

A cewar sanarwar, an kama Ezeokoli Sylva, mai shekara 59 a ranar Juma’a, 29 ga watan Nuwamba, a filin jirgin saman, bayan ya dawo daga birnin Sao Paulo na Brazil a jirgin Ethiopian Airlines.

A cewar hukumar, a lokacin da aka ɗauke shi domin a duba jikinsa, sakamako ya tabbatar da cewa wanda ake zargin na ɗauke da wasu abubuwa ɓoye a cikinsa.

Yadda aka gano ɗan kasuwar

Femi Babafemi ya ce a dalilin haka ne aka sanya masa ido domin kasayar da abubuwan, inda ya fito da ƙulli 29 da aka tabbatar da cewa suna ɗauke da hodar iblis mai nauyin gram 700.

Wanda ake zargin ya yi iƙirarin cewa yana da wani kantin sayar da kayayyaki na Afirika a Brazil inda yake sayar da kayayyaki da suka haɗa da takalma da tufafi.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta dakatar da dan majalisa, ta fadi laifinsa

Ya ce wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa ya sayo hodar ne a Sao Paulo saboda sayarwa a Najeriya da nufin tara maƙudan kudi domin bunƙasa kasuwancinsa.

Jami'an NDLEA sun kama ƙwaya a gidan sanata

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta bayyana dalilin da Sanata mai wakiltar Kwara ta Kudu, Oyeyola Ashiru ke neman a rufe ta.

Shugaban NDLEA ya bayyana cewa jami’an hukumar sun kama miyagun kwayoyi a gidan dan majalisar da ke wakiltar Kwara ta Kudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng