Ana Batun Kudirin Haraji, Shehu Sani Ya ba Shugabannin Arewa Shawara

Ana Batun Kudirin Haraji, Shehu Sani Ya ba Shugabannin Arewa Shawara

  • Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya jawo hankalin shugabannin Arewa kan matsalolin da ke addabar yankin
  • Sanata Shehu Sani ya buƙaci shugabannin yankin da su ba da fifiko wajen samar da ilmi domin tunkarar ƙalubalen da ke addabar Arewa
  • A cewar tsohon sanatan na Kaduna ta Tsakiya, jahilci ne ya haifar da matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Shehu Sani, ya ba shugabannin Arewa shawara.

Shehu Sani ya yi kira ga shugabannin Arewa da su ba ilimi fifiko domin tunkarar ƙalubalen da ke addabar yankin.

Shehu Sani ya ba shugabannin Arewa shawara
Shehu Sani ya bukaci shugabannin Arewa su ba ilmi fifiko Hoto: Shehu Sani
Asali: Twitter

Ya yi wannan kiran ne a wurin taron yara mata na Kaduna 2024 wanda ƙungiyar Creative Think Tank Group ta shirya, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a ofishin gidan rediyon Najeriya, an gano abin da ya faru

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar tsohon sanatan, jahilci ne ya jawo matsalar rashin tsaro a yankin Arewacin Najeriya.

Wace shawara Shehu Sani ya ba da?

"Matsalar da muke fama da ita a yau ba za ta kai wannan matakin ba, da mun ɗauki ilimi da muhimmanci. Arewacin Najeriya yana koma baya a fannin ilimi."
"Idan mutane suka yi ilimi, za su samu ƙarfin gwiwa, ƴanci, al’umma ta samu tsaro, kuma za a tabbatar da zaman lafiya. Idan akwai jahilci, za a samu talauci, idan akwai talauci, sai a samu rashin tsaro."
"Yadda masu faɗa a ji na siyasa ke tunani ba shine mafita ga yankin ba, kamar idan babu man fetur da haraji ba ba za mu iya rayuwa ba."

- Sanata Shehu Sani

Shehu Sani ya caccaki gwamnatin Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yi tir da yadda gwamnatin tarayya ta gurfanar da kananan yara gaban kotu.

Kara karanta wannan

'Babu yadda za a yi shugabancin Najeriya ya dawo hannun mutanen Aewa," Okupe

Sanatan ya ce gwamnatin tarayya ta tafka abin kunya idan aka yi duba da karancin shekarun yaran da ake zargi da aikata laifi lokacin zanga-zanga.

Shehu Sani ya ƙara shawartar gwamnati da ta tabbatar da an mayar da dukkanin yaran gaban iyayensu a jihohin da aka ɗauko su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng