CBN Ya Shirya Share Hawayen Ƴan Najeriya, Ya Taso Bankuna kan Takardun Naira
- Babban banki watau CBN ya ja kunnen bankuna su guji ɓoye takardun Naira a daidai lokacin da ake tunkarar bukukuwan karshen shekara
- Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso ya ce daga ranar 1 ga watan Disamba, jami'ai za su fara yawo don duba ATM na bankuna
- Ya yi kashedin cewa duk bankin da aka gano bai zuba kudi a ATM ba, zai fuskanci hukunci mai tsauri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamnan babban bankin Najeriya watau CBN, Olayemi Cardoso ya yi wa bankuna kashedi kan take doka da kuma ɓoye takardun Naira.
Cardoso ya ja kunnen bankuna ne a wurin wata liyafa da CIBN ta shirya a jihar Legas da ke Kudu maso Yammacin Najeriya ranar Juma'a.
Ƙarancin Naira: CBN ya taso bankuna a gaba
Gwamnan CBN ya ce duk bankin da suka kama yana aikata laifin ɓoye takardun kudi, zai fuskanci hukunci daidai da abin da ya aikata, Daily Trust ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara ƙarancin kudi a hannun jama'a, wanda ya sa masu sana'ar POS suka fara ƙara kudin cajin cire kudi.
Ƴan Najeriya da dama sun nuna takaici ganin yadda ake rasa kudi a na'urorin cire kudi ATM na bankunan kasuwanci.
Sai dai Gwamnan CBN ya yi gargaɗin cewa daga ranar 1 ga watan Disamba, jami'an babban bankin ƙasa za su fara yawo don duba na'urorin ATM.
CBN ga faɗi matakin da zai ɗauka
“Daga ranar 1 ga Disamba, 2024, duk bankin da ya gaza samar da kudi ga kwastomominsa kan kowane irin dalili, zai fuskanci hukunci mai tsauri.
"Za mu fara zuwa bincike a ATM na bankuna don tabbatar da cewa akwai kudi a cikinsu, kuma duk bankunan da suka gaza sa kudi a ATM za mu hukunta su."
"CBN zai ci gaba da sa ido kan harkokin gada-hadar kudi don samar da isassun takardun Naira ga ƴan Najeriya musamman saboda zuwa karshen shekara."
- Olayemi Cardoso.
Wani mai POS, Abdulbasi Salisu ya shaidawa Legit Hausa cewa gaskiya ko da an fara karancin kuɗi to bai zo yankinsu ba a karamar hukumar Ɗanja da ke Katsina.
"Gaskiya ba zan ce maka babu wannan matsalar ba amma mu dai kam ba ta zo mana nan ba tukunna, banki suna bamu abin da muka bukata.
"Sannan cajin da muke yi yana nan bamu ƙara ba, babu dalilin da za mu ƙara saboda mutane na cikin wahala, ko dan haka ya kamata mu tausaya, ta abinci kawai ake yanzu."
CBN ya yi magana kan tsofaffin kuɗi
A wani rahoton, kun ji cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya yi magana kan amfani da tsofaffin takardun kudi a kasar nan.
CBN ya yi magana ne bayan an fara ce-ce-ku-ce kan halascin amfani da tsofaffin takardun kudi a tarayyar Najeriya.
Asali: Legit.ng