Gobara Ta Tashi a Shahararriyar Kasuwa a Jihar Legas, Ta Yi Barna
- Wata gobara ta tashi a fitacciyar kasuwar Ebute Oro da ke jihar Legas a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya
- Gobarar wacce ta tashi da sanyin safiyar ranar Asabar ta lalata shaguna masu yawa da dukiyoyin jama'a
- Hukumar kashe gobara ta jihar wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin ta bayyana cewa ba a samu asarar rai ba kuma jami'anta sun daƙile yaɗuwarta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - An samu tashin gobara a shahararriyar kasuwar Ebute Ero da ke jihar Legas.
Mummunar gobarar wacce ta tashi ta lalata shaguna da dama a kasuwar.
Gobara ta tashi cikin kasuwa a Legas
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar ranar Asabar, 30 ga watan Nuwamban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gobarar ta shafi wani ɓangare na kasuwar da ke kusa da ofishin ƴan sanda da gadar Carter a tsibirin Legas.
Me hukumomi suka ce kan lamarin?
Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Legas, Margaret Adeseye, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar.
Sai dai ta ce an hana gobarar yaɗuwa zuwa sauran wurare, tare da shawo kan lamarin bayan da jami’an kashe gobara suka kai ɗauki.
Ta ƙara da cewa ba a samu asarar rai ba a sakamakon tashin gobarar, amma ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano adadin shagunan da abin ya shafa da kuma ƙiyasin asarar da aka yi.
Karanta wasu labaran kan gobara
- Gobara ta lakume azuzuwa a Niger, an zargi mashaya tabar 'wiwi' da sanadinta
- 'Yan kasuwa sun buga asara mai yawa yayin da gobara ta babbake wata kasuwar Jos
- Kwamitin binciken gobarar tankar fetur a Jigawa ya mika rahotonsa ga gwamnati
Gobara ta tashi a ofishin ƴan sanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata mummunar gobara ta tashi a hedikwatar rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma.
Gobarar wacce ba a iya tantance musabbabi tashin ta ba, a safiyar ranar Asabar ta ƙone ofisoshi shida a hedikwatar rundunar ƴan sandan.
Asali: Legit.ng