'Abin da Ya Sa Ake Zaune Lafiya a Kano Duk da Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma'

'Abin da Ya Sa Ake Zaune Lafiya a Kano Duk da Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma'

  • Gwamnatin Kano ta ce jihar na zaune lafiya ne saboda matakan da take ɗauka da kuɗin da take warewa a bangaren tattara bayanan sirri
  • Shugaban hukumar ayyuka na musamman, AVM Ibrahim Umaru (mai ritaya) ne ya faɗi haka bayan kare kasafin kudi a majalisar dokoki
  • Ya yabawa jami'an hukumomin tsaro da ƴan sa'kai bisa namijin ƙokarin da suke yi wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta faɗi matakin da ta ɗauka da suka ƙara dawwamar da zaman lafiya a faɗin jihar.

Darakta Janar na hukumar ayyuka na musamnan a gidan gwamnatin Kano, AVM Ibrahim Umaru (Mai ritaya) ya ce zaman lafiyar da ake a jihar ba abin mamaki ba ne.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta sauya magana, ta fadi mamallakin shinkafar 'Tinubu' da aka kama

Abba Kabir Yusuf.
Gwamnatin Kano ta ce ba za ta yi sakaci da ɓangaren tattara bayanan sirri ba Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Abin da ya sa Kano ke zaune lafiya

Ya ce Kano na zaune lafiya ne sakamakon kuɗin da gwamnati ke warewa ɓangaren tattara bayanan sirri, kamar yadda Leadership ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ibrahim ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kadan bayan kare kasafin kudin hukumar a harabar majalisar dokokin jihar.

Ya jaddada muhimmancin samar da isassun kudade a ɓangaren tsaro domin dorewar kokarin da ake yi na samar da dawwamammen zaman lafiya a jihar.

Yadda Kano ke kokarin kare kanta

Ibrahim Umar ya ce gwamnati na yin duk mai yiwuwa don tabbatar da matsalolin tsaron da ake fama da su a jihohin Arewa maso Yamma ba su shiga Kano ba.

"Muna ɗaukar matakn kariya, mai girma gwamna ya biyo hanyar da majalisar tsaro za ta riƙa sanin duk bayanan sirrin da ya dace."
"Shiyasa kuka ga mun ware maƙudan kudi a bangaren tattara bayanan sirri don tabbatar da babu wata matsalar tsaro da za ta shigo Kano ba tare da mun ɗauki matakin magance ta ba."

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 10 tana rufe, Gwamna ya bude wata babbar kasuwar dabbobi

"Jami’an tsaro da ƴan sa'kai suna iya bakin kokari wajen wanzar da zaman lafiya da tabbatar da cewa harkokin tattalin arziki na tafiya ba tare da tangarda ba,” in ji shi.

Cin hanci: Gwamna Abba ya tsaya da kafarsa

Rahoto ya gabata cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce ya tsaya da ƙafarsa yayin da shugabannin yan kwadago suka ziyarce shi.

Abba Kabir Yusuf ya ce ba yadda za a yi shugaba ya yi yaki da cin hanci da rashawa ba tare da ya tsaya da kafafunsa ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262