A Karo na Biyu, Tsohuwar Ministar Najeriya Ta Zama Shugabar WTO Ta Duniya

A Karo na Biyu, Tsohuwar Ministar Najeriya Ta Zama Shugabar WTO Ta Duniya

  • Tsohuwar ministar kudi a Najeriya, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta sake ɗarewa kujerar shugabancin kungiyar WTO karo na biyu
  • Ƙungiyar kasuwanci ta duniya ta tabbatar da haka a wata sanarwa da ta fitar ranar Juma'a, ta ce naɗin na biyu zai fara aiki daga 1 ga watan Satumba, 2025
  • Okonjo-Iweala ita ce ƴar Afurka ta farko kuma mace ta farko a tarihi da ta shugabanci kungiyar WTO ta duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ƙungiyar kasuwanci ta duniya (WTO) ta sake nada tsohuwar ministar kuɗi ta Najeriya, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin Darakta Janar a zango na biyu.

A watan Satumba, 2024, Okonjo-Iweala ta sanar da shirinta na sake neman shugabancin kungiyar WTO karo na biyu.

Ngozi Okonjo-Iweala.
Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta sake komawa matsayin shugabar WTO karo na biyu Hoto: @wto
Asali: Twitter

Yadda WTO ta sake naɗa Dr. Ngozi

Shugaban majalisar gudanarwa, Ambasada Petter Ølberg na ƙasar Norway ya sanar da ƴan WTO cewa babu wanda ya nemi gwabzawa da Ngozi kafin wa'adin 8 ga watan Nuwamba ya cika.

Kara karanta wannan

"Akwai lauje cikin nadi": Sanata Ndume ya fadi abin da ya hango kan dokar haraji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyar WTO ta tabbatar da sake naɗa Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a karo na biyu a wata gajeruwar sanarwa da ta wallafa a shafin X ranar Juma'a.

A cewar kungiyar kasuwancin ta duniya, wannan naɗin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Satumba, 2025.

"Majalisar gudanarwa ta naɗa Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin Darakta-Janar karo na biyu, daga ranar 1 ga watan Satumba, 2025," in ji sanarwar.

Yadda ake naɗa shugabar ƙungiyar WTO

Bisa al'ada, ana naɗa shugabar ƙungiyar kasuwancin ne bisa yarjejeniya tsakanin kasashe 166 na kungiyar WTO.

Okonjo-Iweala ita ce mace ta farko kuma 'yar Afirka ta farko da ta shugabanci kungiyar WTO.

Ta samu zarcewa zango na biyu ne ba tare da hamayya ba, babu wani ɗan takara da ya fito da nufin ya kara da ita.

Bola Tinubu ya naɗa ɗan MKO Abiola

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya nada ɗan marigayi Moshood Abiola (MKO) muƙamin hadiminsa na musamman a gwamnatinsa.

Mai girma Tinubu ya nada Jami'u Abiola a matsayin hadimi a bangaren yarurruka da harkokin kasashen waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262