Badakalar N80.2bn: Kotu Ta Yi Fatali da Bukatar EFCC a Shari'ar Tsohon Gwamnan Kogi
- Kotun tarayya ta ɗage zaman sauraron shari'ar tsohon gwamnan jihar Kogi saboda rashin halartar lauyoyinsa yau Juma'a
- Kotu ta yi watsi da bukatar lauyan EFCC, wanda ya nemi a ci gaba da zaman shari'ar duk da babu ko ɗaya daga cikin lauyiyinsa
- Mai shari'a Nwite ya ce hakan ba zai yiwu ba domin ba ayi masa adalci ba, ya ba da lokaci a sanar da lauyoyin wanda ake ƙara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta yi fatali da bukatar hukumar EFCC na gurfanar da Yahaya Bello ba tare da lauyoyinsa ba.
An tsara tsohon gwamnan zai yi jawabi a gaban mai shari’a Emeka Nwite kan tuhume-tuhume 19 da ake masa masu alaka da karkatar da N80.2bn.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa a zaman kotu na yau Juma'a, babu ɗaya daga cikin lauyoyin Yahaya Bello da ya halarci kotun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
EFCC ta shigar da buƙata a gaban kotu
Duk da haka lauyan hukumar yaƙi da cin hanci watau EFCC, Mr. Kemi Pinheiro, SAN, ya roƙi kotu ta ƙyale wanda ake tuhuma ya yi bayani tun da ya gurfana a gabanta.
Ya shaidawa kotu cewa doka ta tanadi cewa wanda ake ƙara ake bukata a wurin shari'a ba dole sai da luyansa ba.
Menene ya hana lauyoyin Bello zuwa kotu?
Da aka tambaye shi dalilin rashin zuwan lauyoyinsa, Bello ya shaida wa kotun cewa ya samu labarin za a yi zaman ne da misalin karfe 11 na daren ranar Alhamis.
Tsohon gwamnan ya kara da cewa mai yiwuwa lauyoyinsa ba su san cewa ƙarar, wadda aka ɗage zuwa ranar 21 fa watan Janairu, 2025, an matso da ita yau ba.
Kotu ta yi fatali da bukatar EFCC
A takaitaccen hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Nwite, ya ce ba zai tilastawa wanda ake kara shigar da bayani kan tuhumar da ake masa ba a lokacin da lauyoyinsa ba sa gaban kotu.
Alkalin ya ba da umarnin sanar da lauyoyin wanda ake ƙara daga nan zuwa zama na gaba a ranar 13 ga watan Disamba, 2023, rahoton Daily Trust.
Tsohon gwamna ya musanta tuhumar EFCC
A wani rahoton, an ji cewa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya musanta dukkanin zarge-zargen almundahana 16 da hukumar EFCC ke masa.
Jami'an EFCC sun yi nasarar gurfanar da Yahaya Bello a gaban babbar kotun tarayya da ke Maitama bisa zargin karkatar da N110bn.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng