Jami'an Hukumar DSS Sun Cafke Dan Gwagwarmaya a Kano
- Jami'an hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) sun cafke wani ɗan gwagwarmaya mai suna Zubair Zubair a jihar Kano
- Lauyan Zubair ya bayyana cewa jami'an na DSS sun tsare shi kafin daga bisani suka miƙa shi ga ƴan sanda a birnin tarayya Abuja
- Haruna Magashi ya bayyana cewa bai san tuhumar da ake yi masa ba amma suna zargin cafke shi na da alaƙa da rawar da ya taka a zanga-zangar #Endbadgovernance
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa, Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun kama wani fitaccen ɗan gwagwarmayar da ke zaune a Kano, mai suna Zubair Zubair.
Zubair Zubair, wanda ya riƙa sukar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, jami'an DSS sun kama shi a Kano sannan aka kai shi birnin tarayya Abuja.
Jami'an DSS sun cafke ɗan gwagwarmaya
Tashar Channels tv ta rahoto cewa lauyan da ke wakiltar Zubair, Haruna Magashi ya tabbatar da cafke ɗan gwagwarmayar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haruna Magashi ya bayyana cewa jami'an hukumar DSS ta kai wanda yake karewa zuwa hedkwatar ƴan sandan Najeriya da ke Abuja.
"A jiya ne hukumar DSS ta kama Zubair a Kano. Da farko dai jami’an DSS sun tsare shi, amma sai suka miƙa shi ga ƴan sanda a Abuja."
- Haruna Magashi
Meyasa aka cafke ɗan gwagwarmayar?
Lokacin da aka tambayi Haruna Magashi kan dalilin cafke ɗan gwagwarmayar, sai ya ka da baki ya ce bai da masaniya kan tuhumar da ake yi masa.
"Har yanzu ba mu tabbatar da tuhumar da ake yi masa ba. Sai dai muna zargin hakan yana da alaƙa ne da irin rawar da ya taka wajen gudanar da zanga-zangar #Endbadgovernance da yadda yake sukar gwamnati mai ci a yanzu."
- Haruna Magashi
Jami'an DSS sun cafke tsohon ɗan takarar gwamna
A wani labarin kuma, kun ji cewa Jam'iyyar PDP ta yi ikirarin cewa hukumar tsaro ta farin kaya watau DSS ta cafke ɗan takarar gwamnan jihar Ogun a inuwar PDP a zaben 2023, Ladi Adebutu.
Sakataren yada labarai na PDP a jihar Ogun, Kayode Adebayo, ya tabbatar da kama Adebutu tare da tsare shi a wata sanarwa da ya saki a birnin Abeokuta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng