"Ku Ceto Mijina:" Uwargidan Kusa a APC Ta Nemi Dauki Kwanaki bayan 'Sace' Shi
- Iyalan wani jigo a jam'iyyar APC sun shiga tsaka mai wuya bayan zargin jami'an tsaro sun biyo dare sun sace mai gidan
- Edith Thomas, mai dakin Charles Kurobo ta sanar da jama'a cewa wasu mutane sanya da kayan 'yan sanda sun kutsa gidansu
- Ta roki Sufeto Janar na Najeriya, Kayode Egbatokun, da sauran masu fada a ji da su taimaka wajen ceto maigidanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Bayelsa - Uwargidan daya daga cikin kusoshin jam’iyyar APC a jihar Bayelsa, Edith Thomas, ta bukaci gwamnati da rundunar yan sanda su kawo masu dauki.
Misis Edith Thomas ta zargi wasu jami’an tsaro, da su ka hada da ‘yan sanda da jami’an NSCDC sun shigo gidansu da misalin 12:00 na dare, aka dauke mai gidanta, Charles Kurobo.
Legit.ng ta wallafa cewa matar ta kara da cewa lamarin ya afku akalla mako guda da ya wuce, a 19 Nuwamba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An 'sace' jagoran jam'iyyar APC a Bayelsa
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa ana zargin wasu jami’an tsaro da dauke Charles Kurobo, wanda ya yi suna wajen sukar manufar shirin afuwa na shugababan kasa (PAP).
Mista Kurobo sananne ne wajen sukar yadda ake gudanar da kwangilar kula da bututun mai da Tantita Security Company ke yi.
An ruwaito cewa kamfanin, mallakin tsohon shugaban kungiyar tsageru, Government Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo ne.
An nemi daukin ceto kusa a APC
A zantawarta da manema labarai, mai dakin Charles Kurobo ta roki Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, da gwamnan Bayelsa, Sanata Douye Diri, su ceto mijinta.
“Da muka leka daga tagarmu da aka lalata, mun ga wadanda suka zo sanye da kayan ‘yan sanda, wasu kuma suna sanye da kayan hukumar tsaro ta farar hula. An zo da jerin gwanon motoci, yawansu ya kai kusan 15."
An samu rabuwar kai a jam'iyyar APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu 'yan jam'iyyar APC sun zargi Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume da nuna wariya ga wadanda su ke ba 'yan kabilarsa ba a Arewa.
Shugaban kungiyar APC a shiyyar Arewa ta Tsakiya, Saleh Zazzaga ya bayyana cewa kusoshi da dama a a yankin sun lura da yadda Sanata George Akume ke samawa 'yan kabilarsa mukami.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng