"Mun Haramta Hayaniya," Gwamnatin Legas Ta Rufe Babban Wurin Ibada da Wasu Otel
- Gwamnatin jihar Legas ta kara rufe wani cocin RCCG, gidan burodi da otal saboda karya dokar kare muhalli da hayaniya
- Hukumar kula da muhalli ta jihar Legas watau LASEPA ce ta ce ba za ta ɗagawa duk wani wanda ya karya doka ƙafa ba
- Shugaban hukumar, Dr. Babatunde Ajayi, ya buƙaci mazauna su bi dokar kare muhalli sau da ƙafa domin gudun matsala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Hukumar kula da muhalli ta jihar Legas (LASEPA) ta garƙame cocin RCCG, otel-otel da wasu wurare saboda damun jama'a da hayaniya.
Jami’an hukumar ne suka gudanar da aikin tabbatar da bin dokar kiyaye hayaniya a Mushin, Amuwo Odofin, da Okota Isolo duk a jihar Legas.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da hukumar LASEPA ta wallafa a shafinta na manhajar X yau Alhamis, 28 ga watan Nuwamba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Legas ta rufe wurare saboda hayaniya
Hukumar ta ce rufe waɗannan wurare ya kara tabbatar da kudirin LASEPA na samar da yanayi mai kyau da inganta mahallci ga dukkan mutanen Legas.
Wuraren da hukumar ta kwace tare da garƙame su, sun haɗa da, gidan burodi, cocin RCCG, kamfanin Gak Universal Allied da otal daban-daban.
A cewar hukumar, an rufe wuraren ne saboda rashin bin ka’idojin muhalli, duk da gargaɗin da LESEPA ta yi a kwanakin baya.
"Babu wanda zamu ɗagawa ƙafa a Legas" - LASEPA
Da yake jawabi kan lamarin, shugaban LASEPA, Dr. Babatunde Ajayi ya ce hukumar ba za ta ɗagawa kowa kafa ba matukar ya take dokar hayaniya.
Ajayi ya ce:
"Kare muhalli ya rataya a wuyan kowa, a matsayinmu na hukuma ba za mu yi ƙasa a guiwa ba wajen tabbatar da bin dokar muhalli.
"Hayaniya da ajiye abubuwa masu haɗari a wuraren da bai dace ba suna jawo wa mutane matsala, don haka muna kira ga ƴan kasuwa da ɗaiɗaikun mutane su bi doka."
Gwamnan Legas ya dakatar da hadiminsa
Rahoto ya gabata cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos ya fatattaki hadiminsa a bangaren kafofin watsa labarai.
Wannan na zuwa ne bayan dakataccen hadimin ya yi magana kan cafke waɗanda ake zargi a zanga-zangar EnSARS a 2020.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng