"'Yan Siyasa Na Shan Wuya": Shugaban Majalisa Ya Mika Kokensa gaban Gwamna
- Shugaban majalisar dokokin Taraba, John Kizito Bonzena, ya nuna damuwa kan halin da ƴan siyasa suke ciki a jihar
- John Kizito Bonzena ya buƙaci Gwamna Agbu Kefas da ya waiwayi tsofaffin ƴan siyasar jihar saboda suna shan wahala
- Shugaban majalisar ya kuma shaidawa gwamnan cewa a shirye tsofaffin ƴan siyasar suke wajen ba da goyon bayansu ga gwamnatinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Taraba - Shugaban majalisar dokokin jihar Taraba, John Kizito Bonzena, ya miƙa ƙoƙon bararsa ga Gwamna Agbu Kefas.
Shugaban majalisar dokokin ya buƙaci Gwamna Agbu Kefas da ya duba halin da manyan ƴan siyasa ke ciki a jihar.
Ƴan siyasa na shan wuya a Taraba
John Kizito Bonzena ya bayyana hakan ne lokacin ƙaddamar da sabon ginin majalisar dokokin jihar, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Agbu Kefas da takwaransa na jihar Adamawa Umaru Fintiri sun halarci wajen ƙaddamar da sabon ginin na majalisar dokokin.
John Kizito Bonzena ya bayyana cewa tsofaffin shugabannin majalisar da tsofaffin ƴan majalisar da sauran ƴan siyasa suna shan wahala.
"Mai girma gwamna, tsofaffin shugabannin majalisa, tsofaffin ƴan majalisa da sauran ƴan siyasa na shan wahala. Suna son taimakawa shirye-shiryenka kuma sun shirya goya maka baya. A taimaka a duba su ranka ya daɗe."
"Muna farin ciki da shirye-shiryenka. Yadda ka gyara ginin majalisarmu abin a yaba ne. Hakan zai ba mambobinmu ƙwarin gwiwar gudanar da ayyukansu cikin farin ciki."
- John Kizito Bonzena
Me Gwamna Kefas ya ce a wajen taron?
Gwamna Agbu Kefas bai yi jawabi ba a wajen taron ƙaddamar da sabon ginin na majalisar dokokin ba.
Sai dai, takwaransa Gwamna Fintiri a lokacin da yake ƙaddamar da ginin, ya godewa gwamnan kan gyara majalisar.
Shugaban majalisa ya ba PDP shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Suleiman, ya bayyana abin da jam'iyyar PDP ke buƙata domin sake dawowa kan madafun ikon ƙasar nan a 2027.
Shugaban majalisar dokokin ya jaddada cewa zaman lafiya da haɗin kai su ne abin da babbar jam’iyyar adawa ta PDP ke buƙata domin ƙwace mulki a hannun Bola Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng