Tsugunne ba Ta Kare ba: EFCC Za Ta Sake Gurfanar da Yahaya Bello a gaban Kotu
- Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) za ta sake gurfanar da Yahaya Bello a gaban kotu
- EFCC za ta gurfanar da tsohon gwamnan na jihar Kogi ne a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja kan badakalar N80.2bn
- Tsohon gwamnan dai na fuskantar tuhume-tuhume 19 a gaban kotun kan zargin almundahana da karkatar da kuɗaɗen jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) za ta sake gurfanar da Yahaya Bello a gaban kotu.
EFCC za ta sake gurfanar da tsohon gwamnan na jihar Kogi ne a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, a safiyar ranar Alhamis.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa za a gurfanar da Yahaya Bello ne a gaban mai shari’a, Emeka Nwite, kan tuhume-tuhume 19 da ke da alaƙa da badaƙalar N80.2bn.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta umarci cafke Yahaya Bello
Idan dai ba a manta ba a ranar 17 ga watan Afrilu, mai shari’a Nwite ya bayar da sammacin kamo tsohon gwamnan sakamakon rashin gurfana a gaban kotu.
Ƙokarin da jami’an EFCC suka yi na aiwatar da umarnin kama Yahaya Bello a Abuja, ya ci tura bayan gwamnan jihar Kogi, Ahmed Ododo, ya tafi da shi a motarsa.
A halin da ake ciki, duk da cewa an ɗage sauraron ƙarar a babban kotun tarayya har zuwa ranar 21 ga watan Janairun 2025, amma hukumar EFCC ta shawo kan mai shari’a Nwite da ya rage ranar.
EFCC za ta gurfanar da Yahaya Bello
Waɗanda za a gurfanar tare da tsohon gwamnan sun haɗa da ɗan uwansa, Ali Bello da wasu mutane biyu, Dauda Suleiman da Abdulsalam Hudu.
EFCC ta yi zargin cewa waɗanda ake tuhumar sun aikata laifukan almundahana, zamba, cin amana da karkatar da kuɗaɗen jama’a.
Yahaya Bello ya dura ofishin EFCC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya dura ofishin hukumar yaki da cin Hanci da rashawa ta EFCC kan zargin almundahana.
EFCC na bincike kan zargin da ake yi wa Yahaya Bello na karkatar da sama da Naira biliyan 100 na kudaden jihar Kogi a lokacin da yake mulki.
Asali: Legit.ng