"Ina da Kwarin Guiwa a Kansa," Gwamna Ya Naɗa Ɗan Uwansa na Jini a Babban Muƙami
- Gwamnan jihar Delta, Sherrif Oborevwori ya ɗauko ɗan uwansa na jini, ya naɗa shi a matsayin shugaban hukumar wasanni
- Oborevwori ya bayyana cewa yana da ƙwarin guiwar ɗan uwansa zai jagoranci hukumar wajen bunkasa harkokin wasanni a jihar
- Ɗan uwan mai girma gwamna, Onoriode Joshua Oborevwori ya kasance tsohon ɗan kwallon kafa da ke goyon bayan wasannin mata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Delta - Gwamna Sheriff Oborevwori ya naɗa ɗan uwansa na jini, Onoriode Joshua Oborevwori a muƙamin gwamnati a jihar Delta.
Gwamna Oborevwori ya amince da naɗin ɗa uwansa a matsayin sabon shugaban hukumar wasaanni ta jihar da ke Kudu maso Kudancin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da gwamnatin jihar Delta ta fitar kwanan nan a birnin Asaba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ya ba ɗan uwansa muƙami a Delta
An tattaro cewa Gwamna Oborevwori ya bayyana kwarin guiwar ɗan uwansa yana da gogewar da zai jagoranci hukumar wajen bunkasa harkokin wasanni.
Wannan naɗin da gwamnan ya yi na zuwa ne bayan shekara guda da karewar wa'adin Chief Tonobok Okowa, wanda ya shafe shekaru takwas a matsayin shugaban hukumar.
Dalilin naɗa ɗan uwan gwamna a muƙami
Oborevwori ya ce:
"Wannan nadin wani ɓangare ne na kudirin gwamnati na bunkasa harkokin wasanni da kuma ba matasanmu dama har su ci nasara a harkokin wasanni daban-daban."
Sauran ƴan majalisar gudanarwa na hukumar sun haɗa da fitattun mutane irin su tsohon dan wasan kwallon kafa na duniya, Sam Sodje, Oghale Ofremu, da Herrita Ehiabor.
Taƙaitaccen bayani game da Joshua Oborevwori
Ɗan uwan gwamnan, Onoriode Joshua Oborewovori ya kasance tsohon dan wasan kwallon kafa kuma mutum ne da yake goyon bayan kwallon kafar mata.
Shi kadai ne mai daukar nauyin kungiyar kwallon kafa ta mata, 'Delta Babes' da kuma ƙungiyar Allstars.
Gwamna ya roki addu'a daga malamai
Rahoto ya gabata cewa Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta ya nemi alfarmar malaman addini wurin taya shi da addu'o'i a gwamnatinsa.
Gwamna Oborevwori ya bayyana haka ne a gidan gwamnati inda ya ce ba zai lamunci ayyuka marasa inganci ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng